Wata gobara da ta tashi a daya daga cikin cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da ke birnin Karachi na kasar Pakistan, wadda ta afku a safiyar yau, ta kashe akalla mutane 11 tare da jikkata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Kamfanin labaran IRNA na kasar Iran ya bayar da rahoto daga kafofin yada labarai na Pakistan cewa, a safiyar yau ranar Asabar, gobarar ta tashi ne daga hawa na shida na ginin, ta kuma bazu zuwa wasu sassa na kasa.
A cewar rahoton na ‘yan sanda, wannan gobarar ba ta da alaka da ayyukan ta’addanci ko barna.
Jami’an asibiti a Karachi sun sanar da cewa mutane 11 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gobarar ta yau.

Source: ABNAHAUSA