‘Yan daba dauke da makamai sun mamaye harabar kungiyar kwadagon Nijeriya (NLC) a jihar Kaduna.
Bata garin dauke da makamai sun kai kimanin 100 dasuka mamaye sakatariyar, wacce ita ce wurin taron masu zanga-zangar da ke shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 5.
Amma jami’an tsaro sun dakatar da ‘yan daban da tarwatsa su, yayin da aka yi nasarar kama 20 daga cikinsu.
Kungiyar kwadago ta zargi gwamna nasiru el rufa’i da laifin turo bata gari domin bata musu gamgamin lumana bisa doka da suka shirya domin kwato ma ma’aikata ‘yanci a jihar da kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da kamun, yana mai cewa an tura jami’an tsaro don kaucewa karya doka da oda.
Daily trust ta ruwaito cewa zanga-zangar ta rikide zuwa rikici a ranar Laraba lokacin da ’yan daba suka far wa masu zanga-zangar a hanyar NEPA da ke kan hanyar Ahmadu Bello Way.
Zanga-zangar ta ci gaba a ranar Laraba yayin da masu zanga-zangar suka hallara a sakatariyar, suna waka, “Babu ja da baya! ba sallama! ”
An tabbatar da cewa gwamna nasiru el rufa’i bayan bata gari da yayi haya domin lalata zanga zangar lumanar ya kuma yo hayar wasu mata domin suyi wata zanga zangar da zata kishiyanci ta kungiyar kwadagon amma sai dai wannan shirin nasa bai kai ga nasara ba.