Babban mai tsara ayyukan binciken duniyar wata na kasar Sin Wu Weiren, ya ce Sin na gaggauta kammala muhimmin burin ta, na aikewa da ‘yan sama jannati zuwa duniyar wata nan da shekarar 2030.
Wu Weiren, wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da kafar CMG, gabanin bikin ranar samaniya ta kasar Sin, wadda aka yi bikin ta a jiya Litinin.
Yanzu haka shekara guda ke nan, tun bayan da hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Sin, ta bayyana shirin kasar na kaddamar da zango na 4, na aikin binciken duniyar wata, wanda ya kunshi harba taurarin dan Adam 3, masu lakabin Chang’e-6, da Chang’e-7 da Chang’e-8, tare da gina tashar kasa da kasa ta binciken duniyar wata a doran watan. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)