Wani masanin harshe kana farfesa a fannin harsuna ya bayyana bambancin da ke tsakanin harshe da wariyar launin fata.
Ana yawan samun wariya ga ɓakar fata daga masu amfani da harsunan Ingilishi da Espaniya
Baki da farar fata – mabambantan launuka ne. Fari, yana nuna alamar haske, sannan ya hada ire-iren launuka da ake da su, a daya bangaren baki na nufin rashin haske da launi.
Fahimtar mu game da baƙi da fari bai wuce tsantsar hasashe ba, la’akari da cewa ƙwaƙwalwarmu ce take fassara abubuwan da aka aika mata.
Da zarar ta gane, mu kawai fassara su za mu yi tare sanya musu suna, amma kowanne muna danganta shi da abubuwa daban-daban.
Ana danganta launin ja da ƙauna da soyyaya da kuma ƙarfi da jarumtaka da haske, shi kuma launi kore yana nuna bege da sa’a da kuma yanayi.
Launin fari yana da alaƙa da salama da ban gaskiya da tsarki da tsabta da kuma haske da annuri, kuma ana danganta ayyukanmu daidai da yanayin da aka suffanta waɗannan launuka, misali ana zaman lafiya da salama yana tafiya da launin farin tuta ko farar Kurciya, kuma mata sukan sanya fararen tufafi idan za su aure.
A gefe guda kuma, baƙar fata yana da alaƙa da tsoro da mutuwa da duhu da ɗaci.
Ma’anar Baki A Kamus Din Ma’anoni
Idan muka duba ma’anar fari da baƙi a cikin ƙamus, ma’anarsu ta farko tana nufin launukan da suke nunawa, sai dai ga jinsi waɗanda suma kamar yadda ake banbanta launuka da ko wanne irin yanayi suma suna da nasu.
Kwatancen da ke tsakanin farin fata da baƙar fata sun bi sahun yanayin kwatancen da ake danganta launuka da kuma daɗaɗɗen tarihin ɓatanci da ake yi kan launin jinsi wanda ke ci gaba da rage ƙimarmu na jinsi da kuma matsayin yadda ake kallonmu a duniya.
Duk waɗannan ma’ana ko matsayi suna wanzuwa ne ta hanyar harshe,
A harshe Ingilishi da Sifaniya, ana ci gaba da nuna wariya ga baƙar fata ta hanyar fahimta da kuma ƙima da darajar da ake danganta launin da shi.
Irin wannan wariya ba wai kawai tsantsar fahimta ba ce ta launi, ta hada matsayin da ke kewaye da nuna kyamar jinsi da ƙabilanci wanda ya danganta baƙar fata da tashin hankali ko bala’i da ɓatanci da rashin bin doka da kuskure a fannin siyasa da tilastawa da bauta da ƙazanta da kuma aikata laifuka.
Hada jerin bayanan da za su samar da wadanan ma’anar ba karamin aiki ba ne, amma wasu misalai za su iya nanu fahimtar da ake da shi kan wariya da muke danganta baki cikin rashin sani.
Muna amfani da kalmar ‘Black sheep’ baƙar dabba a matsayin (daya daga cikin dangin da ya keɓe kansa ko kuma watsar da shi), baƙar kasuwa tana nufin (kasuwa ta haramtacciyar hanya), Black list na nufin (jerin sunayen mutane ko cibiyoyin da ake ɗauka masu haɗari ko abokan gaba), Black Magic, baƙin sihiri na nufin (saɓanin farin sihiri), baƙin taro na nufin (bikin da ake bauta wa Iblis maimakon Ubangiji).
A harshen spaniya, juya baki (“ponerse negro”) yana nufin yin datti ko fushi, ban da haka, akwai sharuɗɗan kamar baƙar ruwa ( dattin ruwa ),baƙar rijiyar ( rijiya mai zurfi), baƙar littafi na wasan kwaikwayo nufin (labarin da ya shafi laifuffuka).
Kalmomi irin su “trabajar en negro” (aiki irin na litattafe), sai kuma kalmar “trabajar como un negro” (aiki kamar bawa), da “trabajo de negro” (bautar da bawa) duk suna da alaƙa kai tsaye da bayi baƙaken fata a lokacin mulkin mallaka.
Duk da alamu sun yi nuna cewa an mance da dalilan da suka haifar da waɗannan fahimtar, amma batun yafi daukar hankali idan aka zo kan launin fata, musamman ƴan kabilar raza negra na Espanya ko kuma Baƙaken fata da ke amfani da harshe Turanci.
Misali, siyakin maganar ‘mutanen da ba fararen fata ba’ ma kaɗai yana nuna wariyar launin fata tare da kabilanci. Amma sai ake nuna kamar ana girmama mutanen ne, amma a bayan fage ana kokarin kare martabar fararen fata.
Yanayin rashin cikakkiyar ma’anar kalmar ta nuna wariyar launin fatar ya sa ana ta kara kirkiro wasu sunan, irin su Afro-American da ke nufin ‘yan Amurka ‘yan asalin Afirka da ‘yan yankin Caribbean wadanda asalinsu ‘yan Afirka ne da sauransu.
Ana amfani da wadannan kalmomin ne a yanzu domin nuna asalin mutum ba ma launin fatarsa kadai ba.
Amma ai matsalar ba ta yadda muke kallon bakaken mutane ba ce, matsalar ita ce yadda muke kallon junanmu baki daya. Wato yadda muke kallon duk wani abu da ya shafi bakaken fata baki daya.
A irin nan ne yanayin tunaninmu a game nuna wariyar launin fata ke fitowa karara, kuma a irin wadannan lokutan ne amfani da kalmomin suka fi nuna bambancin launin fatar.
A Turancin Ingilishi, ana amfani da kalmomin Negro ne domin nuna bambancin launin fata da wariya da cin fuska, sannan yanzu lamarin ya kai suna nuna kyama ko abin kunya.
Wannan shi ya sa ake dan dari-darin amfani da kalmomin, wanda hakan ya sa ake kiransu da kalmomin N, wato N-word, wanda tana cikin kalmomin da suka fi muni wajen nuna wariyar launin fata da cin fuska a Turancin Ingilishi.
Turancin Ingilishi na da kalmar da ke nufin baki ba tare da cin fuska ba, amma a wasu wuraren suma din suke nufin cin fuskar. Ana amfani da su a hakaikaice wajen cin fuska cikin ruwan sanyi.
A harshen Spain, kalmar negro kawai suke da ita, duk da cewa sukan yi amfani da wasu kalmomi irin su mulato da moreno. Ana amfani da kalmar negro domin cin fuska ko kuma hakanan kawai ba da wata manufar ba.
Ana juya kalmar ta koma negrito ko negrita domin nuna kauna, har ma’aurata sukan yi amfani da su misali -mi negro, mi negra-, ba tare da la’akari da launin fatar wanda ke maganar ba ko wanda ake yi wa maganar ba.
Misalin wannan shi ne yadda fitacciyar mawakiyar kasar Ajantina kuma mai fafutikar kwato hakkin mutane, Mercedes Sosai ta yi fice da sunan “La Negra* duk da cewa ba bakar fata ba ce.
A wasu wuraren kuma, kalmar negro na nufin kalmomin N-word ne, amma ba ta kai karfi da zafin cin fuskar wadancan ba.
A kamus na harshen Spain, ana gane cin fuska da nuna wariyar launin fata ne ta ma’ana da kuma manufar mai maganar, ba kai tsaye ba.
Amma a Turancin Ingilishi, wariyar launin fata da ke kunshe a cikin kalmomin N-word a zahiri suke ba sai an tsaya duba ma’ana ba saboda su kansu suna nufin wariyar ce.
Shin hana amfani da kalmomin N-word ya sa Turawan Amurka da Birtaniya sun daina nuna wariyar launin fata? Wannan a bayyana take cewa ko kadan babu abin da hanin ya kawo.
Shin hakan na nufin masu amfani da harshen Ingilishi sun fi na Spain nuna wariyar launin fata? Ba na tunanin wannan tambayar tana bukatar amsa domin nuna wariyar launin fata na ta’allaka ne da manufa da kuma yadda aka jefa ta, kuma manufar ba za ta taba zama daya ba.
Shin wani zai iya fin wani zama mai nuna wariyar launin fata? Shin wani zai iya fin wani zama mai gaskiya?
Daina amfani da kalmomin N-word na nuna cewa kawar da kalmomin kadai ba za ta kawar da nuna bambancin ba.
Fahimtar kalma a matsayin mai dan sauki-sauki, misali kiran mutum mai launin fata ko kuma ta cin fuska irin su kalmomin N-word a lokuta da dama suna danganta ne da yanayi da manufar magana.
Akwai yiwuwar kalmar da aka fara amfani da ita da manufar cin fuska, a karshe ta zama ba ta cin fuskar ba, ko kuma ta faro da rashin cin fuska ta kare da manufar cin fuska. Wannan ke nufin kalmomi masu dan sauki-sauki za su iya rikidewa su zama na cin fuska.
A ra’ayina, bai kamata a takaita yaki da nuna wariyar launin fata da yunkurin kawar da wata kalma ko wasu jerin maganganu ba kawai. Tacewa tare da hana amfani da su ba za su taba magance matsalolin ba.
Hana amfani da wasu kalmomin harshe ba shi da wani amfani idan har akwai manufar nuna wariyar a zukatar mutane, domin za su nemo wasu hanyoyin da za su rika nuna bambancin a tsakaninsu.
Ya kamata ne a mayar da hankali wajen wayar da kan mutane muhimmancin girmama juna. Wannan ne zai sa mu yi watsi da hanyoyin da muke bi wajen nuna bambancin wariyar launin fata.
Abin da ke faruwa wajen amfani da wadannan kalmomin da ma wasu shi ne muna amfani da son rai ne wajen amfani da su. Harshe tamkar madubin al’umma ce. Ba za a magance wata matsala ba ta hanyar fasa madubin, maganin matsalar ita ce a gyara ta yadda kallon madubin zai rika bayyana mana abubuwa masu kyau.
A karshen Karni na 19, fitaccen masanin nan na kasar Cuba mai suna Jose Marti ya rubuta wata makala, inda a ciki ya ce, “Mutum ya wuce a tsaya ana siffanta shi da wani farin fata ne ko bakin fata.”
Ya kara da cewa, “Duk wani abu da ke jawo bambancin a tsakanin mutane, ko yake raba tsakaninsu, ko yake raba abubuwan da suka shafe su, wannan laifi ne babba ga al’umma.”
Duba Nan: Dakatar Da Wasu ‘Yan Majalisu A Zamfara
Idan lokacin da dukkanmu muka gane wannan, to daga lokacin duk wata kalma da za mu yi amfani da ita wajen kiran kanmu da ita ba ta da amfani. Amma kafin wannan lokacin ya zo, ya kamata mu sani cewa a yanzu lallai kalmomin da muke amfani da suna da tasiri.