A wasannin gasar cin kofin Afrika da ke gudana a kasar Kamaru, Equatorial Guinea ta bayar da mamaki bayan da ta lallasa Algeria mai rike da kofin gasar da ci 1-0 a wasan da suka hadu a jiya Lahadi, a zagaye na biyu na rukunin E.
Esteban Obiang ne ya zura kwallo daya tilo a wasan a minti na 70 da fara wasan.
Wannan rashin nasara ita ce ta farko da ‘yan wasan kasar Aljeriya suka yi bayan wasanni 35 da suka yi fice ba tare da an doke su ba.
A halin yanzu dai Equatorial Guinea ta samu maki ukun farko a wasanta da Aljeriya, bayan da a wasanta na farko ta sha kashi a hannun Ivory Coast da ci 1-0.
A wasa na biyu a safiyar jiya , Ivory Coast da Saliyo sun tashi 2-2.
Matsayin kungiyoyi na biyar bayan kammala zagaye na biyu:
1- Ivory Coast da maki 4
2- Equatorial Guinea da maki 3
3- Saliyo da maki biyu
4- Algeria da maki daya
Kamaru tana karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 33 tsakanin ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, tare da halartar kungiyoyi 24, kuma kungiyoyi 16 ne za su samu tikitin zuwa zagaye na gaba.