Zinedine Zidane ba zai horar da wata kungiya a wani lokaci na kusa ba saboda zai jinkirta har sai an samu gurbi a babbar tawagar kwallon kafar kasar Faransa, a cewar jaridar Libertad Digital.
A watan da ya gabata Zidane ya rabu da Real Madrid, yana mai bayyana rashin aminci da yarda, da rashin zumunci mai inganci a kungiyar a matsayin dalilansa na ajiye aiki.
Mai horar da tawagar kasar Faransar, Didier Deschamps ya ce ba shi da niyyar barin tawagar Faransa a wani lokaci a nan kusa, sabida haka Zidane zai yi zaman dakon lokacin da dan talikin zai yi hannun riga da tawagar.
A wani labarin na daban hankulan masu sharhi da sauran masu bibiyar kwallon kafa sun koma kan dakon ganin zabin da kungiyar Real Madrid za ta yi na wanda zai maye gurbin kocinta Zinaden Zidane da ya yanke shawarar ajiye aikinsa a daren ranar Laraba.
Zidane ya kawo karshen aikinsa ne bayan jagorantar Real Madrid wajen lashe manyan kofunan da suka hada da na gasar zakarun nahiyar Turai 3 a jere, sai kuma kofunan gasar La Liga 2.
Sauran kofunan da Zidane ya lashewa Real Madrid a zamanin da ya horas da kungiyar sun hada da na gasar Spanish Super Cup 2, babbar gasar turai ta European Super Cup 2, da kuma kasar zakarun kungiyoyin duniya ta Club World Cup guda biyu.
A halin yanzu dai wadanda ake sa ran kungiyar ta Real Madrid za ta zaba don maye gurbin Zidane sun hada da tsohon kocin Juventus Massmiliano Allegri, Antonio Conte da shi ma jiya a ajiye aikinsa da Inter Milan, sai kuma Raul Gonzalas, tsohon tauraron kungiyar ta Real da a yanzu yake horas da kungiyar ta Castilla ajin matasa.
Tun a shekarar 2018 ne dai aka alakanta Allegri da kulla yarjejeniya da Real Madrid lokacin da Zidane ya ajiye aikinsa a karon farko, kafin ya sake karbar ragamar jagorancin Madrid din a shekarar 2019.
Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka Inter Milan da Juventus ne neman kulla yarjejeniya da shi Allegri.
A yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace makomar aikin horas da Real Madrid da kuma ta masu horaswar uku da ake alakantawa da kulla yarjejeniya da kungiyar.