Zainab, mai shekaru 30 da haihuwa, kuma tana da ‘yaya uku, ta bar aikinta na ma’aikaciyar jinya a shekarar 2021 don cim ma burinta na sanya hijabi tare da kungiyar kwallon rugby ta kasar Ingila.
“Na daina aikin jinya…
Na yanke shawarar zama bakar fata Musulma mace ta farko da ta fara bugawa Ingila wasa,” kamar yadda ta shaida wa shafin intanet na Olympics.
Matar Musulma ta fara buga wasan Rugby tana da shekaru 14, godiya ga daya daga cikin malamanta na Sakandare, inda nan take ta shaku da juna.
Wasa a cikin tawagar rugby ta kasa ba abu ne mai sauki ba ga mace musulma da ta rike hijabi kuma ta cika burin addini da al’adunta.
Zainab ta ce: Wannan ita ce shawarar da na yanke a rayuwata, na shiga duniyar da ban sani ba. Amma ban yi nadama ba, na fi jin gamsuwa.