Hukumar kwallon kafar Nijeriya NFF, ta ce tawagar ‘yan wasan kasar ta Super Eagles za su fafata da takwarorinsu na Ghana a wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da kasar Katar za ta karbi bakunci, a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abuja kuma a cewar sanarwar ta NFF za a yi wannan karawar ce a ranar 27 ga watan Maris.
A halin yanzu ana dakon sanarwa daga hukumar kwallon kafar Ghana, kan zagayen farko na wasan neman cancantar da za su buga, wanda ake sa ran ya gudana ko dai a ranar 23 ga watan na Maris ko kuma a ranar 24 ga watan.
Baya ga wasan Nijeriya da Ghana, Jadawalin wasannin neman tikitin halartar gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Katar ya nuna cewa Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowace kasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.
A sauran wasannin neman tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya a Katar, Kamaru za ta kara da Algeria, sai Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da za ta fafata da Morocco.