An kawo karshen gasar cin kofin nahiyar Turai jiya Lahadi, inda Italiya ta bada mamaki wajen lashe kofin wanda shine na biyu a tarihinta.
Italiya ta doke Ingila mai masaukin baki ne a bugun fenariti da ci 3-2 a wasan karshe da suka kara a Wembley a gaban ‘yan kallo kimanin dubu 60, bayan da aka tashi wasa kunnen doki 1-1.
Mai tsaron ragar Ingila ya yi kokarin tare kwallaye har biyu a bugun Finaretin, amma hakan bai basu nasara ba, sakamakon barar da kwallaye har uku a bangarenta ta hannun Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka.
Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta rusa damar ta na dauka kofin da take jira tsawon shekaru 55.
Ingila ce ta fara cin kwallo ta hannun Luke Shaw kuma haka aka tafi hutun rabin lokaci, bayan komawa zagaye na biyu ne Italiya ta farke ta hannun Leonardo Bonucci. Kuma aka Karkare 1-1, kafin a kara musu lokaci, har zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga.