Ita Atletco Madrid ta yi nasarar daukar kofin La Liga na bana, bayan yadda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Real balladolid da ci 2-1 a wasan mako na 38 na karshe a kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021 a kasar Spaniya.
Dan wasa Luis Suarez ya kasance cikin hawaye ranar Asabar bayan kwallon da ya ci ya taimakawa Atletico Madrid daukar kofin La Ligar, yana mai godiya ga kungiyar da ta cece shi.
Dan wasan dan kasar Uruguay, wanda ya koma Atletico Madrid daga Barcelona a watan Agusta, ya gode wa Atletico Madrid yadda ta bude masa kofofinsu bayan Barcelona ta nuna cewa bashi da amfani a cewarsa.
Real Madrid da Barcelona da Sebilla sukayi na biyu da na uku dana hudu, kuma suka samu tikitin gasar Zakarun Turai na Champions League a kakar wasa mai zuwa ta shekarar 2021 zuwa 2022.
A gasar Premier Ingila kuwa, kungiyar kwallon kafa t Manchester City ce ta lashe kofin na bana, bayan da Manchester United ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Leicester City a Old Trafford tun a satin daya gabata, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar.
Manchester City ce ta yi ta daya a kakar bana sai Manchester United ta biyu a teburi, sannan Liverpool ta uku da Chelsea ta hudun da za su wakilci Ingila a Champions League a kakar badi.
Seria A – Italiya
kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan tayi bikin lashe kofin Seria A na bana gaban magoya banya na cikin gida, bayan doke Udinese da ci biyar da 1 a wasan karshe da aka fafata a ranar Lahadi.
Inter Milan ce tayi na daya a bana, sai abokiyar hamayyarta wato AC Milan ta biyu a teburi, sannan Atalanta ta uku sai kuma Jebentus da ta sha dakyar wajen samun tikitin zuwa Champions League mai zuwa.
Bundesliga – Jamus
Bayern Munich ce ta lashe kofin, a matsayin ta daya a saman teburi, sai Leipzig ta biyu sannan Dortmund ta uku sai kuma Wolfsburg ta hudu a wadanda zasu wikilci kasar a zakarun Turai ta badi.
Ligue 1 – Faransa
A gasar Ligue 1 na kasar Faransa kuwa kungiyar kwallon kafa ta Lille ta sha gaban PSG ta lashe kofin na bana, yayin da PSG da Monaco da Lyon suka samu tikitin wakiltar kasar a gasar zakarun Turai ta badi, a matsayin na daya zuwa na hudu.