Wataƙila De Gea ya yi ritaya, Kloop ya yi watsi da tayin Jamus
Mai yuwuwa mai tsaron raga David de Gea, wanda yanzu haka ba shi da ƙungiya tun bayan barinsa Manchester United a wannan kaka, ya yi ritaya idan har bai samu tayi ba daga wata babbar ƙungiya ba. Golan na ƙasar Sifaniya na da shekara 32. (Guardian)
Cristiano Ronaldo, na ƙoƙarin ganin yadda zai jawo tsohon abokin wasansa a Manchester United De Gea zuwa Al Nassr, amma ɗan wasan kamar ya fi son zama a Turai. (90min)
Kyaftin ɗin Arsenal Martin Odegaard, mai shekara 24, ya samu damar tafiya Tottenham a lokacin da yake tasowa, amma kuma sai wata waya da ya samu daga Zinedine Zidane ta sauya hakan. (Mirror)
Tsohon ɗan wasan tsakiya a Ingila Jesse Lingard, mai shekara 30, zai soma atisaye da Al-Ettifaq bayan ƙungiyarsa ta Nottingham Forest ta sallame shi a watan Yuni. (Fabrizio Romano)
Barcelona na da yaƙinin Atletico Madrid za ta nemi yuro miliyan 80 kan ɗan wasan Portugal mai shekara 23 Joao Felix da ke zaman aro a Nou Camp zuwa yarjejeniyar dindindin, yayin da Manchester City za ta nemi yuro miliyan 25 kan ɗan wasan baya Joao Cancelo, mai shekara 29. (Mundo Deportivo)
Ɗan wasan AC Milan Francesco Camarda mai shekara 15 ya ɗauki hankalin Manchester City da Borussia Dortmund saboda iya zura ƙwallonsa. (Calciomercato)
Wakilin ɗan wasan tsakiya a Ecuador Moises Caicedo ya ce matashin mai shekara 21 na son zuwa Chelasea, duk da cewa Liverpool na son gabatar da fam miliyan 111 kan ɗan wasan na Brighton, yayin da Chelsea ke son ganin ta janye shi tun a watan Janairu. (Sport Italia)
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi watsi da tayin karɓan aikin koci a Jamus kafin ƙasar ta koma ga Julian Nagelsmann domin jagorantarsu a wasan Yuro 2024. (Telegraph)
Ɗan wasan Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 24, na nuna takaici kan yadda abubuwa ke kasancewa a Bayern Munich a wannan kaka. (Bild daga Mail)
Newcastle United na cikin ƙungiyoyin da ke bibiyar ɗan wasan Southampton Carlos Alcaraz mai shekara 20. (Talksport)
Tottenham za ta saurari tayin da ake gabatar mata kan ɗan wasan tsakiya Giovani lo Celso, mai shekara 27. (Football Insider)
Manchester United na ƙoƙarin sake riƙe Hannibal Mejbri, ɗan wasanta mai shekara 20, da sabon kwantiragi (90min)