An takaita hakan in ban da a manyan wasannin gasar Premier League da kuma wasannin karshe na kofin FA da kuma Carabao sai dai tsohon kyaftin din na Arsenal kuma mai horar da Crystal Palace Patrick Vieira ya ce ana wasa da muhimmancin da adawa da nuna wariyar ke da shi, domin a cewarsa abu ne da ya kamata a karfafa yi a maimakon yi masa rikon sakainar kashi ba.
”Yana da muhimmanci a ci gaba da saka kafa a kasa domin nuna adawa da nuna wariya don duk muna adawa da hakan kuma yaki ne da zai dauki tsawon lokaci ana yi a don haka dole mu ci gaba da saka gwuiwa a kasa,” in ji Vieira.
A watan Fabrairun shekara ta 2021 ne dan wasan gaban Crystal Palace Wilfried Zaha ya daina dabi’ar saka gwiwa a kasa, inda ya kafa hujja da cewa yin hakan bai sauya komai ba domin har yanzu da dama daga cikinsu na fuskantar wariyar launin fata.
An samo dabi’ar ne daga wani dan wasan kwallon zari rugar Amurka Colin Kaepernick a ranar 1 ga watan Satumban shekara ta 2016, don nuna adawa da wariyar launin fata da cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa bakake a kasar sa.