Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA, Aleksander Ceferin ya ce yana na fatan za’a iya bullo da tsarin mafi karancin albashi a fagen kwallon kafar Turai, inda ya ce dukkanin kungiyoyin sun amince kan batun.
Ceferin ya ce ya yi magana da hukumar tarayyar Turai game da batun kuma an tattauna kan kawo irin wannan matakin sannan ya ce manyan kungiyoyi, kananan kungiyoyi, kungiyoyin kwallon kafa da ke karkashin kulawar gwamnati, kungiyoyin manyan ‘yan kasuwa, kowa ya amince.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya yi magana game da yiwuwar samar da tsarin mafi karancin albashi a bangaren kwallon kafa a watan Maris din daya gabata.
“Ba wai muna maganar wadanda suka mallaki kungiyoyi ba ne, ana maganar darajar gasar ne, domin idan har kungiyoyi biyar za su ci nasara a kodayaushe to babu ma’ana kuma,” in ji shugaban UEFA.
Ya ci gaba da cewa “Amma dole ne ya zama yarjejeniya ta gama gari kowacce da zata kunshi kowacce gasa da kuma UEFA, domin idan muka yi shi kuma sauran kungiyoyin ba su yi ba, to hakan ba shi da ma’ana.
Ya ce a yanzu, suna da sabuwar doka bayan shekara ta 2024 cewa za a iya kashe kusan kashi 70 na kudaden shiga domin biyan albashi da hada-hadar ‘yan wasa, amma hakan bai wadatar ba saboda idan kudaden shiga sun kai biliyan biyar, kashi 70 na da yawa.
Saboda haka wannan ita ce ci gaba a nan, kuma ba ya jin tsoron masu kungiyoyin kwallon kafa domin UEFA ce ke jagorantar gasar Turai kuma suna da kyakkyawar alaka da hadakar kungiyoyin wasanni a halin yanzu.