Yayinda aka dawo domin ci gaba da buga wasannin UEFA Champions League a zagaye na biyu.
BBabbn wasan da masu sha’awar kallon kwallon kafa zasu fi mayar da hankali a wannan satin shi ne wasa tsakanin Real Madrid da Napoli.
A tarihi, kungiyoyin biyu sun hadu sau biyar inda Real Madrid ta samu nasara a wasanni 4 sannan akayi kunnen doki daya.
Kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke kasar Italiya bata taba samun nasara akan Real Madrid ba.
Kungiyar Napoli ce ke jan ragamar rukunin C na gasar ta UEFA yayinda Madrid ke binta a baya.
Madrid tana da ‘yan wasan da suka samu rauni kuma ba zasu buga wasan na yau ba da suka hada da Militao, David Alaba da kuma mai tsaron raga Thiabaut Courtois.
A wani labarin na daban an kece raini tsakanin Dan Aliyu da Rabe Shagon Ebola a wasan safiyar Lahadi a Marabar N’yanya jihar Nasarawa a wasan da aka fafata a gidan damben Bambarewa sarkin yakin masu gidajen dambe a kasar nan.
An kuma yi wasannin ne da aka yi wa ‘yan damben Arewa biyo ajo, wato Sha’aike da Shamsu Dogon Autan dan Bunza kuma Dan Aliyu daga Arewa da Rabe daga Kudu sun sha kida daga makadin ‘yan dambe Labaran dan Gwamba, wanda ya yi musu kurarin da ya ba su karfin shiga fili.
Turmin farko ba wanda ya kai duka haka ma a turmi na biyu, daga baya ne suka sa kuzari a turmi na uku, amma ba kisa aka raba su sannan sauran wasannin da aka buga a ranar ta Lahadi Boloko da Shagon Lawwalin Gusau, turmi biyu suka yi ba kisa.
Shi kuwa Shagon Na Aisha nasara ya yi a kan Shagon Na Jafaru Kura a turmin farko sannan an kuma yi canjaras tsakanin Autan Na Aisha da Garkuwan Dunan Ba-ta-Jemu ba, amma ‘yan damben sun samu kudi sosai daga ‘yan kallo,domin sun yi wasa mai kyau.
Shi ma wasan Garkuwan Kurma da Shagon Bokan Sama’ila ya kayatar sosai, sannan aka kammala da wasa tsakanin Shagon Basiru da Dogon Inda sannan duk da haka an kuma sa kudi a wasa tsakanin Rabe da Autan Na Aisha, amma wani dan kallo ya hana damben cewar Autan Na Aisha kada ya yi wasan.
Abinda kuwa ya faru shi ne an bukaci ya bayar da kudi fiye da wanda aka sa, shi kuwa bai yi hakan ba, inda ‘yan kallo wadanda suka bukaci yin dambe suka kara kudi amma daga karshe dai ba yi damben da kowa ya so ya kashe kwarkwatar ido ba.