Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, ya tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa kakar wasa ta shekara ta 2024 kamar yadda kungiyar ta amince kuma shima ya amince da yarjejeniyar.
Tun farko Tuchel mai shekara 47 ya sanya hannu kan yarjejeniyar watanni 18 ne a lokacin da ya maye gurbin Frank Lampard a watan Janairun wannan shekarar bayan kungiyar PSG ta kore shi kuma shi ne ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin Zakatarun Turai na Champions League da kuma kammala kakar bana a mataki na hudu a teburin Premier.
“Akwai abubuwa masu yawa da za su zo nan gaba kuma muna hankoron ganinsu cike da zumudi saboda haka zamu ci gaba da ganin mun samu nasarorin da muka saka a gaba,” a cewar Tuchel.
Lokacin da aka naɗda shi, Chelsea na matsayi na tara a teburin Premier tare da yin rashin nasara a wasa biyar kuma dan kasar Jamus din ya ci wasanni 19 cikin 30 da ya jagoranci kungiyar, inda aka ci shi biyar.
A wani labarin na daban gwamnatin najeriya ta haramta amfani da manhajar tuwita a fadin kasar, baya bayan nan an jiyo shugaban kasar muhammadu buhari yana bayyana dalilin da yasa gwamnatin sa ta haramta amfani da manhajar tuwita din.
Mutanen najeriya dake ciki da wajen kasar ta najeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da wanna mataki da gwamnatin buhari ta dauka, inda mafi akasari ke ganin wannan wata takaddama ce da ta shafi iya tsakanin gwamnati da kamfanin na tuwita amma bai kamata a haramtawa sauran ‘yan kasa amfani da manhajar ta tuwita ba.
Koma dai menene al’ummar najeriya basa goyon bayan haramta musu amfani da manhajar tuwita, mafi yawanci suna ganin babbar matsalar najeriya ba wannan bace.
Babbar matsalar najeriya tabarbarewar tsaro ce wacce ta shafi kudanci da arewacin najeria kuma gwamnati ta gaza yin komki a kai.