Tottenham za ta bukaci zunzurutun kudi har Fam miliyan 150 a kan dan wasanta Harry Kane, a cinkin tsabar kudi kawai, ba tare da an hada mata da wani dan wasa ba, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.
Wannan ka’ida na zuwa ne a yayin da Manchester City ta bayyana aniyar mika wa Tottenham manyan ‘yan wasanta biyu, Raheem Sterling da Gabriel Jesus don kai ga gaci a cinikin.
Kane wanda a halin yanzu dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ne na daya daga cikin ‘yan wasan da aka fi nema da ke kasuwa a halin yanzu, bayan da ya saka kwallaye 23, ya kuma taimaka aka ci 14 a kakar da aka karkare kwanan nan.
A wani labarin na daban kuma Eden Hazard ya bayyana farin cikinsa a game da nadin Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin kungiyar Real Madrid, yana mai cewa hakan yana da matukar kyau a gare ni.
Ancelotti ya koma Real Madrid ne bayan da ya yi hannun riga da Everton a karo na biyu a ranar Talata, inda ya sanya hannu a kwantiragin zaman shekaru 3 a Santiago Bernabeu.
Hazard yana sa ran aiki da dan kasar Italiyan, wanda ya maye gurbin Zinedine Zidane, kuma yana jin cewa Real Madrid za ta ba mara da kunya a karkashin jagorancinsa.
Ancelotti ne ya gaji Jose Mourinho a Santiago Bernabeu a shekarar 2013, inda daga nan ne ya lashe kofuna 3 da tawagar a cikin kakar wasa 2, ciki har da kofin Copa del Rey da na FIFA World Club na zakarun kungiyoyin duniya.
Jigo a cikin jerin gudummawar da Ancelotti ya bayar a Madrid shine lashe kofin zakarun Turai na 10, wato La Decima, inda Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan karshe a shekarar 2013-14 don cin kofin a karo na 10.