Tottenham ta ɗauko ɗan Isra’ila Solomon
Tottenham ta kammala daukar Manor Solomon domin buga ya kungiyar a gasar firemiya a kakar wasa mai zuwa.
Dan wasan na Isra’ila ya zama ɗan wasa na huɗu da ƙungiyar ta sayo a wannan bazarar.
Solomon ya haɗe da Dejan Kulusevski da Guglielmo Vicario da kuma James Maddison wajen sanya hannu kan yarjejeniyar dindindin a filin wasa na Tottenham.
Dan wasan mai shekaru 23, wanda ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro a Fulham, ya isa arewacin Landan ne a matsayin ɗan wasan da kwantaraginsa ta ƙare.
Solomon dai ya kulla yarjejeniya da Shakhtar Donetsk har zuwa karshen wannan shekarar amma FIFA ta bai wa duk wanda ba ‘yan asalin ƙasar Ukraine ba da ke wasa a ƙasar damar dakatar da kwantiraginsu.
Solomon ya taka rawar gani yayin da Fulham ta ƙare a mataki na 10 a gasar firemiya kuma kocinta Marco Silva ya so ya ajiye shi.
Ya buga wa Isra’ila wasanni 35 kuma ya zura ƙwallo bakwai a raga tun da ya fara buga wa ƙasarsa wasa a shekarar 2018.
Read More :
Biden ya tona asirin sojojin Amurka.
Moscow: Taron kolin NATO bai yi nasara ba kafin a fara shi.