Tawagar Da Ke Kewayawa Da Kofin Duniya Ta Isa Kasar Senigal Watanni Biyu Kafin Fara Gasar.
A ci gaba da kewayawa da ake yi da kofin zinariya na gasar kwallon kafa na cin kofin duniya a kasashen da suka yankin tikitin halartar gasar ya isa birnin Dakar na kasar Senigal a watanni biyu kafin fara gasar ta cin kofin duniya wanda kasar Qatar za ta dauki bakunci a watan Nuwamban shekara ta 2022 da muke ciki,
Tsohon dan wadan kwallon kafa na kasar Faransa David Trezeguet lokacin da yayi ido biyu da dinbin magoya bayan kungiayr kwallon kafa na kasar sanigal da suka yi masa lale marhabin ya fadi cewa Kasar Senigal a matsayinta ta daya daga cikin kasashen da za’a dama dasu a cikin gasar za ta buga wasanta na farko da Nerharland wanda lamari ne mai wahala, sai dai suka da kwarewar da zasu iya yin nasara a wsan.
Kungiyar kwallon kafa ta Lions of Teranga wadda ke rike da kofin nahiyar Africa. Yana daga daga cikin kasashen 5 da zasu wakilci nahiyar a gasar ta cin kofin duniya , kuma kaftin dinta Sadio Mane da sauran abokan wasansa suna rukunin A ne tare da kasashen Qatar Natheland da kuma Ecodo.
A watan fabererun da ya gabata ne kasar Senigla ta dauki kofi na farko a tarihin gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Africa.