Szymon Marciniak, alkalin wasan da ya jagoranci wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, ya amince cewa ya yi kuskure a wasan da aka yi tsakanin Argentina da Faransa.
Marciniak shi ne alkalin wasan farko daga Poland da ya sa ido kan wasan da ya fi kowanne girma da hatsari a kwallon kafa a duniya a ranar Lahadin da ta gabata.
Daga cikin manyan abubuwan da Szymon Marciniak ya yi sun hada da bayar da bugun fanareti har sau uku sannan kuma ya bawa dan wasan Faransa Marcus Thuram katin gargadi ba tare da neman shawarar VAR ba bayan shi aka gwabje a cikin zagayen da ake buga fanareti.
Sai dai alkalin wasan mai shekaru 41 ya amince da cewa “kuskure ne”
“Tabbas, akwai kurakurai a wannan wasan na karshe,” kamar yadda Jaridar Vanguard ta nakalto daga kamfanin Sport.PL yayin tattaunawarta da alkalin wasan.
A wani labarin Babban dan Sarkin Gumel kuma Ciroman Gumel, Farfesa Lawal Ahmed Sani wanda ya jagoranci tawagar masarautar ta Gumel a madadin Sarkin wajen kai ziyarar ta’aziyya zuwa fadan Sarkin Lakwaja, ya bayyana rasuwar Sarki Kabir Maikarfi a matsayin babban rashi ga al’ummar masarautar da kuma iyalansa.
Ya ce masarautar Gumel ta kadu matuka a yayin da ta samu labarin rasuwar Sarkin Lakwaja, wanda ta bayyana shi a matsayin mutum mai kima da daraja a idonun al’ummarsa da kuma masarautun arewacin Nijeriya a tsawon shekaru fiye da talatin da ya yi a gadon sarautar Lakwaja.