Yayin da ake shirye-shiryen fara wasannin gasar Laliga ta kasar Sifen an bayyana ranar da za a kece raini a tsakanin manyan kungiyoyi Real Madrid da Barcelona.
Wasan da ake wa lakabi da El Clasico shi ne ake hasashen wasa mafi zafi a tsakanin kungiyoyi a harkar kwallon kafa.
Mahunkuntan Laliga sun bayyana ranar 29 ga watan Oktoba 2023 a matasayin ranar da za a buga wasan farko, inda Barcelona za ta karbi bakuncin abokiyar hamayyarta Real Madrid.
Yayin da ranar 21 ga watan Yuni, 2024 Real Madrid za ta karbi bakuncin Fc Barcelona a filin wasa na Santiago Bernabeau da ke Madrid.
Tsawon shekaru El Classico ya zama wasan da mafi yawan masu sha’awar kallon kwallo ke jira don ganin wanda zai samu nasara a kan abokin karawarsa tsakanin Real Madrid da Barcelona.
A wani labarin na daban gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda, ya kira wani taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro domin tattauna hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar tsaro a jihar.
Masu ruwa da tsakin sun hada da shugabannin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, ‘yan majalisar dokokin jihar, shugabannin tsaro, masu rike da sarautun gargajiya da malaman Addini a jihar.
Da yake magana a wajen taron, Gwamna Radda ya ce an kira taron ne domin zakulo hanyoyin magance kalubalen tsaro a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta dauki aniyar kafa wata cibiya ta musamman a cikin al’umma mai suna ‘Community Watch’ da za ta nemo matasa ta ba su horo na musamman don su ba da gudunmuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Wannan cibiya, za ta hada matasan da jami’an tsaro a dukkanin kananan hukumomi 34 da ke jihar wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Radda, ya ce zai gabatar wa majalisar dokokin jihar kudiri domin kafa doka ta musamman da za ta sa a samu raguwar aikata ayyukan assha a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara na jihar.
Inganta tsaro na daga cikin alkawuran da gwamnan ya dauka a lokacin da yake yakin neman zabensa.