Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa sun shirya kare kambunsu na shekara mai zuwa kuma yana da yakinin cewa ‘yan wasansa sun shirya yin hakan a gasa mai zuwa.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce ta lashe kofin Premier League na bana a ranar 11 ga watan Mayu na wannan shekara, ranar da Manchester United ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Leicester City a filin wasa na Old Trafford.
Manchester City ce ta yi ta daya a bana sai Manchester United ta biyu a teburi, sannan Liverpool ta uku da Chelsea ta hudun da za su wakilci Ingila a Champions League a kakar badi.
Ranar 29 ga watan Mayu na wannan Shekara za a buga wasan karshe a gasar zakarun turai ta Champions League tsakanin Manchester City da Chelsea a kasar Portugal a filin wasa na Estadio de Dragoa, wato filin wasa na FC Porto.
Kuma duk wadda ta lashe kofin ba wani karin gurbi da za a bai wa Ingila, tunda kungiyoyin biyu sun samu tikitin buga Champions League a badi kamar yadda sabuwar dokar hukumar kwallon kafa ta turai ta tanadar.
kungiyar kwallon kafa ta Leicester City wadda ta lashe gasar FA Cup ta yi ta biyar a Premier a wanna Shekara da kuma West Ham United ta shida za su wakilci Ingila a gasar Europa League a kaka mai zuwa.
“Muna da kwarin gwiwa sosai wajen ci gaba da jan ragamar gasar firimiyar Ingila kuma za muyi iya yinmu domin ganin mun ci gaba da lashe gasar a nan gaba domin hakan yana cikin tsare tsaren mu” in ji Guardiola
Manchester City wadda ta lashe Carabao Cup a kakar nan, na nufin a kwaskwarimar da aka yi wa gasar zakarun Turai za’a nemi wadda ba ta samu gurbin Europa ba kuma tana da maki da yawa ita ce Tottenham.
Saboda haka Tottenham wadda ta yi ta bakwai za ta shiga wasannin cike gurbi don buga Europa League a badi kenan sai dai abokiyar hamayyarta wto kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta karkare gasar Premier League ta bana a mataki na takwas da maki 61, ba za ta buga gasar Zakarun Turai a badi ba.
Wannan ne karon farko da Arsenal ba za ta wakilci Ingila a gasar zakarun Turai ba tun bayan shekarar 1995 zuwa 1996 haka kuma ta kasa hawa kan Tottenham a teburin Premier tun daga shekarar 2016, Tottenham ce a gaba kafin ka tarar da Arsenal.
Tuni kungiyar Sheffield United ta yanki gurbin buga Championship a badi, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Wolbes ranar 17 ga watan Afirilu ana saura wasa shida a kare kakar bana.
West Brom ce ta bi bayan Sheffield a barin Premier League ta kakar nan, bayan da Arsenal ta doke ta 3-1 ranar 9 ga watan Mayu saiFulham kuwa a ranar 10 ga watan Mayu ta tabbata cewar ita ce ta ukun da za ta koma buga Championship a kakar badi.