Bayanai daga majiyoyi kwarara a Spain sun ce kungiyar Sevilla ta ce a shirye take ta sake kulla yarjejeniyar shekaru 5 da kaftin din kungiyar Real Madrid Sergio Ramos.
Ramos mai shekaru 35 ya taka leda a kungiyar Sevilla ne a ajin matasa kafin sauya sheka zuwa Real Madrid a shekarar 2005, inda kawo yanzu ya shafe shekaru 16 yana haskawa.
Tun a farkon kakar wasan da aka karkare ne dai ake ta cece-kuce kan makomar Sergio Ramos a Real Madrid wanda yarjejeniyarsa da kungiyar ke shirin karewa a karshen wannan wata na Yuni, la’akari da cewa a watanni baya dan wasan ya ki amincewa da tayin sabuwar yarjejeniyar da aka mika masa.
Baya ga kungiyar Sevilla dai, an dade ana alakanta kaftin din na Madrid da komawa kungiyoyin PSG ko kuma Manchester United.
A wani labarin na daban mai tsaron bayan Real Madrid Sergio Ramos ba zai samu damar taka leda a karawar kungiyar ta sa karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai da za ta kara da Liverpool ba, saboda raunin daya samu a kafarsa.
Real madrid na shirin karawa da Liverpool ne ranar 6 ga watan nan a zagayen farko na wasan gab dana kusa da karshe na cin kofin zakarun turai gabanin su sake haduwa a wasa na biyu ranar 14 ga watan.
Jaridun wasannin Spain sun ruwaito Ramos na cewa raunin ya matukar harzuka shi ganin yadda zai rasa haduwar ta cin kofin zakarun Turai da kuma wasan El Classico duk dai a cikin wannan watan wato haduwar Barcelona da Real Madrid.
A shekarar 2018 ne Real Madrid ta yi nasara kan Liverpool bayan zura mata kwallaye 3 da 1 baya ga targada hannun tauraron tawagar wato Mohamed Salah da Ramos ya yi a wancan lokaci dalilin da ya sanya wasu ke kallon haduwar a matsayin ta huce haushi duk da cewa Liverpool din ta yi nasarar dage kofin a 2019.