Saka na daf da saka hannu kan ci gaba da taka leda a Arsenal.
Arsenal na sa ran sanar da kulla yarjejeniya kafin karshen Premier League ta bana da cewar Bukayo Saka ya amince zai ci gaba da wasa a Gunners.
Dan wasan tawagar Ingila, an yi ta alakanta shi da zai koma wasu kungiyoyin Premier da taka leda, yanzu a shirye yake ya kulla kwantiragi da Arsenal.
Saka mai shekara 21 yana cikin fitattun Gunners da suka sa kungiyar ke takarar lashe Premier League na kakar nan.
Ya ci kwallo 13 ya kuma bayar da 11 aka zura a raga, inda Arsenal take ta biyun teburi a fatan da take na lashe kofin babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
Saka ya zura kwallo uku a raga a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, inda tawagar Ingila ta kai daf da na kusa da na karshe a wasannin.
Dan wasan ya saka hannun a kwantiragin ta ci gaba da taka leda a Gunners a 2020, wanda yarjejeniyar za ta karkare a karshen kakar badi.
Bayan da Saka ke daf da kulla yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, watakila Granit Xhaka ya bar Emirates a karshen kakar nan.
A shirye Gunners take ta bar dan kwallon tawagar Switzerland ya koma wata kungiyar, idan an taya shi da tsoka, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2024 a Gunners.