‘Dan wasa Cristiano Ronaldo ya soki Manchester United a wata hira da Piers Morgan ya yi kwanan nan.
Tauraron ya koka kan yadda ake gudanar da abubuwa a kungiyar, yace babu wani cigaban da aka samu yanz.
Ronaldo ya zargi kocinsa da rashin girmama shi, sannan kuma ya maidawa irinsu Wayne Rooney martani.
A wata hira da ya yi da Piers Morgan, ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo ya yi bayanin halin da ya tsinci kan shi.
Jaridar Sun ta fitar da labarin hirar da Piers Morgan ya yi da Cristiano Ronaldo a shirinsa na TalkTV, a nan aka ji ya soki kungiyar da yake bugawa wasa.
Ronaldo ya yi ikirarin abubuwa ba su tafiya daidai a kulob din tun da Sir Alex Ferguson ya ajiye aiki a 2013, ya kuma ce bai ganin girman Eric Ten Haag.
Skysports ta rahoto ‘Dan wasan mai shekara 37 a Duniya yana cewa kocin kungiyar watau Erik ten Hag bai ganin darajarsa, don haka shi ma bai girmama sa.
Wasu ba su son gani na
Ronaldo A game da yunkurin korarsa daga kulob din, Ronaldo yace bayan mai horas da ‘yan wasan kungiyar, akwai mutum biyu ko uku da ke neman ganin bayansa.
“Maganar gaskiya, ban sani ba.
Bai dame ni ba.
Mutane su ji gaskiyar lamari. Kwarai, ina jin an ci amana ta. Wasu ba su so na, ba a bana ba, har a bara.”
Ban san meyasa hakan yake faruwa ba. Tun da Sir Alex Ferguson ban ga canjin da aka samu ba, babu komai.
An kori Solskjaer, an dauko hayar Darekta Misali, abin mamaki ne Man United ta sallami Ole (Solskjaer), ta kawo Ralf Rangnick, mutumin da ba koci ba ne, wannan ya daurewa kowa kai.
Feguson, Rooney da Dawowa Manchester ‘Dan wasan na kasar Portugal yake cewa kaunar da yake yi wa Manchester United ta sa ya dawo kulob din, ya ki yarda ya tafi kungiyar Manchester City. Nayi aiki da abin da zuciyata take so.
Shi Sir Alex Feguson yace mani, ‘Ba za ta yiwu ka tafi Manchester City’, sai na ce ‘To, ‘Yallabai.’ – Cristiano Ronaldo.
A hirar, Ronaldo yace watakila Wayne Rooney yana sukarsa ne saboda shi ya daina kwallo, kuma ga shi idan aka yi maganar kyau, shi kyakkyawa ne.
Shari’ar Greenwood a Ingila A karshen Oktoban bana ne aka ji labari ‘Dan wasan kwallon gaban kungiyar Manchester United, Mason Greenwood zai bayyana gaban kuliya.
Ana tuhumar Greenwood mai shekara 21 da laifin fyade, don haka zai kare kan shi a wata kotu mai zama a Salford a garin Manchester a kasar Birtaniya.
Source:LEGITHAUSA