An dakatar da kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, daga buga wasan neman cancantar shiga gasar Euro 2024 da za su kara da Luxembourg ranar Litinin.
Dan wasan gaban na Al-Nassr ya karbi katin gargadi a wasan da suka doke Slovakia da ci 1-0 a ranar Juma’a.
Alkalin wasa Glenn Nyberg ya zabi nuna katin gargadi ga Ronaldo duk da cewar VAR ta nemi ya duba abinda ya faru amma yaki.
Yanzu dai an dakatar da Ronaldo saboda katin gargadin da ya dauka, shi ne na uku a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.
A wani labarin na daban matashin dan kwallon Barcelona Lamine Yamal ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa tawagar kasar Sipaniya kwallo a karawar da suka yi da Georgia a wasan neman gurbin shiga gasar Euro 2024.
Yamal mai shekaru 16 da kwana 57 ya canji Dani Olmo daf lokacin da za a tafi hutun rabin lokaci.
Yamal ya karbe tarihin dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga wa tawagar Spain kwallo daga Gavi, wanda ke da shekaru 17 da kwanaki 62 lokacin da ya fara buga wa kasar wasa a shekara ta 2021.
Tun can dama matashin dan wasan Yamal shi ne mafi karancin shekaru da ya taka leda a gasar La Liga a Barcelona lokacin da ya fara a watan Afrilu.
Lamine Yamal wanda ya samu yardar kocin Barcelona Xavi ya samu kyautar gwarzon dan wasa bayan ya taimaka aka zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Villarreal da ci 4-3 a watan jiya.
Source: LEADERSHIPHAUSA