Kungiyar kwallon kafa ta AS Roma ta kori Jose Mourinho daga aiki, inda ta tabbatar da cewar tana bukatar yi wa kungiyar garambawul.
Wannan dai na ma zuwa ne bayan da kungiyar ta gaza yin katabus a gasar Serie A, inda ta ke a mataki na tara a teburin gasar.
Mourinho wanda kwantaraginsa zai kare a watan Yunin 2024, ya kulla yarjejeniya da Roma a 2021, inda ya jagoranci kungiyar wajen zuwa wasan karshe na kofin Europa Conference League.
A makon da ya wuce ne aka yi waje da Roma daga gasar Coppa Italia, wanda hakan ya kara fusata mahukunta kungiyar game da Mourinho.
Tuni rahotanni daga Italiya suka bayyana cewar tsohon Kyaftin din kungiyar, wato Daniele De Rossi ne, zai maye gurbin Mourinho a matsayin sabon kocin Roma.
A wani labarin na daban gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ce, gwamnatinsa za ta kafa gidauniyar tattara kudade domin biyan bukatun iyalan jaruman da suka rasu a bakin aiki.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bikin ranar tunawa da sojojin Nijeriya na shekarar 2024 da aka yi ranar Litinin a Kano.
Ya ce, gwamnatinsa za ta gayyaci manyan mutane a jihar domin su mara wa gwamnati baya wajen kafa gidauniyar tallafawan.
A cewarsa, za kuma a yi amfani da gidauniyar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da samar da ayyukan yi ga matasa.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa, Jiharmu ta dore da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma gwamnatinmu ba za ta bar komai a baya ba don aiwatar da wannan kyakkyawar aniyar,” in ji shi.
Da yake jawabi kan iyalan jaruman sojojin da suka rasu, gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen kyautata rayuwarsu.
Ya kuma bayyana cewa, iyalan jaruman da suka rasu, za su ci gajiyar tallafin da za a raba wa al’ummar jihar.
Gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Source: LEADERSHIPHAUSA