Arsenal na dab da amincewa da yarjejeniyar daukar Declan Rice daga West Ham kan fam miliyan 100 kamar yadda rahotanni daga babban birnin kasar Ingila wato London suka bayyana.
Rice, mai shekara 24 kuma dan kwallon tawagar Ingila na iya koma wa Arsenal da tsada, idan aka hada da tsarabe-tsarabe kuma Arsenal din a shirye take ta dauki matashin a matakin mafi tsada da za ta saya a tarihin kungiyar.
Rice, dan kwallon tawagar Ingila wanda ya wakilci kungiyar a wasanni daban-daban ya fara kwallo daga karamar kungiyar West Ham daga baya ya koma babbar kungiyar ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 2016.
West Ham United ta tabbatar cewar Rice zai bar kungiyar a karshen kakar nan kuma dan wasan ya lashe Europa Conference League a bana tare da West Ham, bayan da su ka ci Fiorentina 2-1.
Arsenal, wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League za ta buga Champions League a kaka mai zuwa kuma tana fatan lashe gasar firimiya a kakar wasa mai zuwa.
A wani labarin na daban zakarun gasar Bundesliga na bana Bayern Munich na Duba yiwuwar daukar dan wasan baya na Manchester City Kyle Walker.
Walker wanda ya zo City a shekarar 2017 daga Tottenham Hostpur bai samu damar buga wasan karshe na gasar kofin zakarun Turai wanda kungiyarsa ta lashe bayan lallasa Inter Milan a filin wasa na Ataturk dake kasar Turkiyya.
Hakan na nufin Walker baya cikin Yan wasan da koci Pep Guardiola ke shirin tunkarar kakar badi, Mai shekaru 33 na cikin yan wasanda da Bayern Munich ke sa Ido akansu domin kara karfafa kungiyar.
Walker ya lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya 5, kofin kalubale 2 da kuma gasar zakarun Turai a shekaru 6 da ya shafe a Etihad bayan zuwansa daga Tottenham akan Yuro Miliyan 50 a 2017.