Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke buga gasar Firimiyar Ingila ta nuna sha’awar daukar dan kwallon Ingila kuma kyaftin din West Ham United, Declan Rice wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasanni ta bana.
Arsenal ta na neman kara karfin tawagar ‘yan wasanta domin tunkarar gasar zakarun turai da za ta fafata a badi da kuma neman lashe gasar Firimiya bayan rasa na bana da ta yi a wani yanayi mai ban mamaki.
Declan Rice na daga cikin ‘yan wasan West Ham da ke jiran buga wasan karshe na gasar Uefa Conference League bayan doke kungiyar kwallon kafa ta AZ Alkmar wadda ka iya zama wasansa ta karshe a West Ham.
Rice dai na daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraronsu ke haskawa a nahiyar Turai kuma kungiyoyi da dama na neman ya zama nasu kafin badi.
Daga cikin kungiyoyin Turai da ke neman Rice akwai Man Utd, Chelsea, Arsenal da Bayern Munich ta Kasar Jamus.
A wani labarin na daban shugaban Kasar Brazil, Lula Luiz Da Silva, Ya Bukaci a gaggauta kawo karshen kalaman wariyar launin fata a wasannin kwallon kafa musamman a Turai.
Shugaba Lula ya bayyana haka a shafinsa na twitter, cewar kalaman wariyar launin fata ba za su haifar da da mai ido ba matukar ba’a bar su ba.
jawabin shugaban ya zo ne bayan magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Valencia sun furta kalaman wariyar launin fata akan dan wasan Brazil mai taka leda a Real Madrid, Vinicius Jr.
Alkalin wasa Ricardo Burgos, ya tsayar da karawar bayan an yi masa korafi akan magoya bayan Valencia inda suka dinga jifa suna furta kalaman da basu dace ba akan dan wasan, kuma daga baya ya ba shi katin kora bayan ya bugi dan wasan Valencia, Hugo Duroc, da kusurwar hannunsa.
Shugaban na Brazil ya kara da cewa dole a gaggauta dakatar da faruwar hakan a nan gaba.