Tauraron dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford, ya yi hatsarin mota yayin da yake tafiya gida bayan da kungiyarsa ta doke Burnley da ci 1-0 a ranar Asabar.
Rashford, mai shekaru 25, an ba da rahoton cewa Rashford ya yi karo da wata motar yayin da yake barin filin atisaye na United Carrington.
Rashford ya buga wasa da Burnley, amma ya kasa jefa kwallo a raga a wasan da kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes ya jefa kwallo daya tilo a wasan.
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun isa wurin inda suka kai daukin gaggawa.
Wata majiya ta ce Rashford ya girgiza amma bai ji rauni ba.
Bruno Fernandes, wanda ya zura kwallo daya tilo a Turf Moor, ya zo kan wurin da lamarin ya faru kuma an yi imanin ya tsaya don ba da taimako.
A wani labarin wasannin ka yau Lahadi 24, ga Satunba 2023 za a buga wasan da masu sha’awar kallon kwallon kafa ke kira da London Derby, wato wasa tskanin manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu Arsenal da Tottenham Hotspur.
Wasan yana daukar hankalin masu sha’awar kallon kwallon kafa da ke fadin Duniya.
Duba da cewar dukkan kungiyoyin biyu babu kanwar lasa a cikinsu matukar ana magana ta iya taka leda.
Kungiyoyin biyu wadanda dukkansu suke a babban birnin London na kasar Ingila,sun shahara a fannin kwallon kafa.
Arsenal da Tottenham sun hadu sau 189 a tarihi,inda Arsenal ta samu nasara sau 78 aka yi canjaras sau 51 inda kuma Tottenham samu nasara har sau 61.
Zuwa yanzu Tottenham tana matsayi na biyu da maki 13 yayinda itama Arsenal take da maki 13 a matsayi na hudu akan teburin gasar Premier League ta bana.
Source: LEADERSHIPHAUSA