Rashford na ci gaba da yin wuta a Man United a bana
Manchester United ta ci gaba da zama ta uku a teburin Premier League, bayan kammala karawar mako na 24.
Ranar Lahadi United ta doke Leicester City da ci 3-0 a Old Trafford a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Marcus Rashford ne ya ci biyu a wasan, yayin da Jadon Sancho ya zura na uku a raga da ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.
Rashford ya zama na farko da ya ci kwallo a wasa bakwai a jere a Premier League a Old Trafford, tun bayan bajintar Wayne Rooney a 2010.
Dan wasan ya zura kwallo 17 a bana a gida a dukkan fafatawa, ya zama na biyu bayan Rooney mai 19 a 2011-12.
Dan wasan tawagar Ingila ya zura kwallo 24 a dukkan fafatawa a bana, kakar da yafi yin kwazon zura kwallaye a tarihi, saura wata uku a kammala kakar nan.
Mai shekara 25 ya ci kwallo 17 a wasa 18 tun bayan da aka karkare gasar kofin duniya a Qatar, ba wani dan wasa daga manyan gasar Turai biyar da ya kaishi bajintar.
United, wadda ta tashi 2-2 da Barcelona za ta karbi bakuncin kungiyar Sifaniya a wasa na biyu ranar Alhamis a Old Trafford.
Kungiyoyin biyu na buga karawar neman gurbin shiga ‘yan 16 da za su ci gaba da wasannin Europa League.
United wadda ke cikin FA Cup za ta fafata da Newcastle United ranar Lahadi a wasan karshe a Caraboa Cup a Wembley.