A yau Lahadi aka gudanar da bikin rufe gasar Cin Kofin Duniya ‘Qatar 2022 FIFA World Cup a babban Filin wasan Lusail, birnin Doha.
Bayan fafatawa tsakanin yan kwallon kasar Faransa da kasar Ajantina na tsawon mintuna 120, Ajantina ta samu nasarar lallasa Faransa.
Kamar yadda aka saba, kungiyar kwallon duniya FIFA na bada lambar yabo ga daidaikun yan kwallon da suka taka rawar gani a gasar kofin duniya.
Kyaututtuka hudu ake badawa na wanda yafi cin kwallaye a gasar, mai tsaron gidan da yafi kokari, matashin dan kwallon gasar da kuma Zakaran gasar.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku mutum hudu da samu lambar yabon Qatar 2022: Kyllian Mbappe (Faransa) – Wanda yafi cin kwallaye a gasar (Kwallaye 8).
2. Emilliano Martinez (Ajantina) – Mai tsaron gidan mafi kokari
3. Enzo Fernandez (Ajantina) – Matashin Dan Kwallon gasar Qatar
Lionel Messi (Ajantina) – Zakaran Qatar 2022 Qatar 2022
A wani labarin na daban sabon shugaban kamfanin Twitter, Elon Musk, ya ce yana ganin zai iya ajiye aikin shugabancin kamfanin, bayan shafe wata biyu da zaman akan muƙamin.
Elon ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda yace a kada kuri’ar goyan bayan ya ci gaba da kasancewa a kan kujerar ko a’a, kuma yace zai amfani da abinda kuri’a ta nuna.
A safiyar yau Litinin, awa shida kan a rufe zaben, sakamakon ya nuna ya sauka ya samu kashi 56.3%, kar ya sauka kuma 43.7%.
Tun bayan da ya sai kamfanin kuma ya zama shugabansa a watan Oktoba, sabon shugaban ya fito da shedar tabbacin sahihancin shafi da wasu kaloli maimakon ruwan shuɗi kawai.
Bayan da ya sai kamfanin ya fitar da wasu sabin dokoki da ka’idoji wanda yake ganin sun fi ye masa.
Wanda ya hada da sauke wasu masu múkami da daraktocin kamfanin.
Elon ya kori duk wanda yaga bazai iya bin ƙa’idojin da ya gindaya ba.
Sannan yace sahihancin shafi da ake sawa mutane yanzu ya zama na kudi in kana da shi zaka ringa biyan wasu kudade, yayin da kuma in kana so zaka siya.
Elon ya dakatar da wani zaure da ake tattaunawa a dandalin Twitter (Twitter Space) din sakamakon wata muhawara mai zafi da sukai da mai Kula da zauren.
Yanzu dai abin jira a gani shine ko shi Elon din zai sauka daga mukaminsa bayan kammala zaben ko kuwa.
Elon Musk ya bayyana a shafin sa jin ta bakin mutane kan ya sauka daga mukaminsa ko kuwa ya ci gaba da zama a matsayin shugaban kamfanin.