Premier League; Ronaldo Yaki Halartar Wasannin Atisaye Na Man. United.
Dan wasan gaba na Manchester United, Cristiano Ronaldo, bai koma atisaye ba a ranar jiya Litinin, kamar yadda kungiyar ta tsara cewa kowanne dan wasan zai koma domin fara daukar horo a yau a kokarin tunkarar sabuwar kakar wasa mai zuwa.
A ranar Asabar ne dai Ronaldo ya bayyana cewa yana son barin kungiyar sakamakon kungiyar ba zata buga gasar kofin zakarun turai ba a shekara mai zuwa.
Sai dai kai tsaye kungiyar ta mayar da martani inda ta ce dan wasan bana sayarwa bane kuma tana fatan ya koma daukar atisaye a yau.
Ronaldo, ya bayar da dalilin cewa ba zai koma daukar horon bane a yau sakamakon matsala da iyalinsa, kuma kungiyar ta amince da wannan uzurin nasa.
READ MORE : Burkina Faso; Mutane 34 Ne Suka Rasa Rayukansu A wasu hare-Haren Ta’addaci.
Tuni dai aka fara danganta dan wasan da komawa kungiyoyin Bayern Munchen da Chelsea da Roma da Napoli da kuma tsohuwar kungiyarsa ta Sporting Lisbon ta Portugal.
READ MORE : Iran Da Oman Sun Tattauna A Kan Wasu Batutuwa Da Suka Shafi Gabas Ta Tsakiya.
READ MORE : Sakon Tel Aviv zuwa Yamma; Idan ba ku fuskanci Hizbullah ba, samar da iskar gas ba shi da matsala.