Wasu Kamfanonin dake daukar nauyin wasannin gasar neman cin kofin Turai ta EURO 2020 sun fara nuna damuwa dangane da dabi’ar da wasu fitattun ‘yan wasa keyi kamar irin su pogba, inda suka ce hakan da a Amurka akayi da sai an hukunta ‘yan wasan.
Wannan na zuwa ne bayan da Chiristiano Ronaldo da kuma Paul Pogba suka gusar da kayan sha dake gabansu gabanin amsa tambayoyin ‘yan jaridu.
Paul Pogba
Dan wasan tawagar Faransa, Paul Pogba ya matsar da kwalbar barasa dake gabansa a lokacin da zai gana da ‘yan jaridu, bayan nasarar da suka samu kan Jamus da ci 1- 0 a gasar Euro 2020 ranar Talata, a matsayin gwarzo a wasan.
Ronaldo
Hakan na zuwa bayan da shima Cristiano Ronaldo ya janye kwalaben Coca Cola dake gabansa bayan wasan da Portugal ta lallasa Hungary da ci 3-0.
Matakin Ronalda ya janyo wa kamfanin Cocoa Cola asarar dala biliyan 4 cikin ‘yan sa’o’i, sai dai ya zuwa yanzu babu bayanan asarar da Pogba wanda Musulmi ne ya janyo wa kamfanin barasar.
A wani labarin na daban kungiyar Real Madrid ta sallami kaften dinta Sergio Ramos bayan ya shafe tsawon kakanni 16 yana taka mata tamola, yayin da ta ce, a gobe Alhamis za ta yi masa bikin karramawa kafin ban-kwana da shi baki daya.
Za a karrama gwarzon dan wasan a bikin da zai samu halartar shugaban Real Madrid, Florentino Perez.
Dan wasan mai shekaru 35, ya yi ta fama da rauni a wannan kaka kuma wasanni biyar kacal ya buga wa kungiyar tun farkon wannan shekara.
A jumulce Ramos ya buga wa Real Madrid wasanni 671 tare da jefa kwallaye 101 a kungiyar, inda kuma ya lashe mata kofunan La Liga biyar, da kofunan Gasar Zakarun Turai hudu da kuma Copa del Rey guda biyu.
Ramos da Real Madrid sun gaza cimma matsayar tsawaita masa kwantiraginsa wanda zai kawo karshe a ranar 30 ga wannan wat ana Yuni.