Pele, Dan Kwallon ya rasu ranar 29 ga watan Disambar shekarar bara, kwana goma da kammala wasan cin kofin duniya da akai a kasar Qatar.
Shi ne dan wasa daya tilo da ya ci kofin duniya sau uku a tarihin babbar gasar kwallon.
Hukumar kwallon Kafar duniya FIFA, ta wallafa yawan kwallonsa da suka kai 1,200 da doriya banda wata guda daya daka kashe masa.
Dan wasan kasar Brazil da yai tashe a gasar cin kofin duniya wanda kuma shine sillar shaharar sa.
Tashen nasa ya fara ne daga shekarar 1958 zuwa 1970 dai-dai inda kuma yayiwa yan wasan duniya fintikau.
Jaridar Mirror.co.uk ta rawaito yadda jama’a da dama ke musu kan shin ko shararrun yan wasan nan na yan zu Messi da Ronaldo Zasu Kamo Pele?
To sai dai masu musun sun fara bayar da dalilan da yasa ko Pelen zai zama zakarar duniya, ko kuma su Mesii da Ronaldo zasu tureshi.
Masana na cewa ai shi Pele dan wasan tsakiya ne, inda kuma kusan duk aiyukansa a tsakiya yakeyi, amma su Messi da Ranaldo yan gefe ne kuma a gefe suke kwallonsu.
Kuma indan an sake lura za’a ga dan wasan ya buga kwallonsa a kasar ne a mafi yawan rayuwarsa, amma su kuma su Messi da Ronaldo sun buga mafi yawan kwallayensu ne a kulob – kulob.
Ba Iya Kwallo Pele Keyi Ba Baya ga buga kwallo, Pele ya zama wani zakaran gwaji da yai suna a tsakanin kasashen bakaken fata da suke neman yancin a shekarun 1950 da kuma 1950, domin Pele ya ziyarci kusan kashen Kudancin Amurka gaba dayansu da da kuma masu yawa a nahiyar Africa.
Hatta kasa Nigeria Pele ya zo, dan yana kasar ne ma akai juyin mulkin shekarar 1977 inda juyin mulkin bai nasara ba, amma an kashe shugaban kasa na lokacin wato Janar Murtala Ramat Muhammad.
Yawan Kwallayen Messi Da Ronalado Legit.ng Hausa ta tattaro yawan kwallayen da Pele wanda akewa lakabi da Gwani da kuma Messi da akewa Lakaci da Kura kyaci da gashi da kuma Ronaldo suka ci.
Kulub Pele Ronaldo Messi 1167 701 695 Kasa 118 77 98.