Lakabin Pele da ake fada wa marigayi gwarzon dan kwallon duniya, bisa ka’ida ya shiga cikin kamus, inda yake nufin “zakakuri ko fintinkau ko abu na daban kamar yadda aka tabbatar”.
Kamusun harshen Portugal mai suna Michaelis, daya daga cikin mafi shahara a Brazil, ya sa sunan “Pelé” a matsayin sabuwar kalmar siffa a kundinsa na intanet kuma za’a ci gaba da amfani da kalmar.
Sanya sunan Pele a cikin kamus, ya zo ne bayan wani gangami da gidauniyar Pele ta kaddamar na neman a karrama tauraron dan kwallon, inda ya samu amincewa har mutane fiye da dubu 125,000 suka sa hannu.
Pele dai ya mutu a watan Disamban bara yana da shekara 82 a duniya kuma shi kadai ne dan kwallon da ya ci kofin duniya sau uku, kuma mutane da yawa na daukar sa a matsayin dan kwallon kafa mafi fice a tarihi.
A lokacin sana’arsa ta kwallon kafa tsawon shekara 20, Pele ya ci kwallaye masu yawa a tarihi har guda 1,281 lokacin da ya buga wa kungiyar Santos ta Brazil da kuma a kasar Brazil da kulob din Cosmos na New York.
Tun rasuwarsa, sanadin larurorin da ya yi fama da su na cutar dajin hanji, tsohuwar kungiyarsa Santos da tashar wasanni ta SporTB da gidauniyar Pelé suka yi ta matsa lamba don ganin an martaba sunan tauraron kwallon kafan na duniya, ta hanyar shigar da shi cikin kamus.
A ranar Laraba ne kuma, masu buga kamusun Michaelis suka sanar da cewa za’a shigar da kalmar cikin kundin kalmominsu na intanet a nan take kuma da zarar an zo wallafa kwafin takarda na kamus Michaelis nan gaba za a hada da kalmar pele.
An sanya sunan kamar haka: “pe.lé adj. (siffa) Mutum wanda ya zarce saura, wanda nagartarsa, kima ko fifikonsa ba daya ne da komai ko da kowa ba, kamar dai Pelé, lakabin Edson Arantes do Nascimento, wanda ake dauka a matsayin dan wasa mafi gawurta a tsawon dukkan zamani kuma
zakakuri, mai fintinkau kuma na-daban.”
Gidauniyar Pelé, wadda kungiyar agaji ce da aka kafa don alkinta
tarihin gwarzon dan kwallon, ta ce karramawa ce da ta dace ga Pele kuma
Kalmar tuni ake amfani da ita wajen bayyana mutumin da ya yi fice kan
abin da yake yi, ta shiga shafukan kamus ta wallafa a sakon tuwita.