Victor Osimhen ya yi barazanar kai karar Napoli kan bidiyonsa da suka yada a kafar Tik Tok.
Wakilin Osimhen ya ce dan wasan zai iya kai karar Napoli gaban kotu bayan da aka buga wani faifan bidiyon Osimhen yana bugun fanareti sannan kuma aka goge shi daga shafin kungiyar na TikTok.
Osimhen na Napoli ya taimaka wa kungiyar ta Italiya ta sami nasarar lashe kofin Serie A ta hanyar zura kwallaye 31 a kakar wasan da ta gabata.
Wakilin dan wasan na Najeriya Roberto Calenda ya fitar da wata sanarwa a shafin X yana mai cewa bidiyon ya haifar da mummunan lahani ga dan wasan.
Mun tanadi hakkin daukar matakin doka da duk wani shiri mai amfani don kare Victor inji Calendar.
A wani labarin na daban kuma yunkurin Nijeriya na karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2027 da Jamhuriyar Benin ya ci tura.
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dauka na bai wa kasashen Kenya da Uganda da Tanzania damar daukar nauyin gasar.
CAF ta bayyana hakan ne a karshen taron kwamitin zartarwa da ta gudanar a ranar Laraba.
Kasar Morocco ce ta samu nasarar daukar nauyin gasar ta AFCON a shekarar 2025.
Nijeriya ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa mafi girma a Afirka a shekarar 2000.
Kasar ta dauki nauyin gasar ne tare da kasar Ghana a waccan shekarar.
Source LEADERSHIPHAUSA