Manchester City ta yi rashin nasara a karon farko a kakar wasanni ta bana bayan da Newcastle ta doke ta a filin wasa na St. James Park a gasar League Cup ta bana.
City ta fara wasan ba tare da manyan ‘yan wasanta ba kamar Ederson, Haaland, Bernado Silva da Kyle Walker ba.
Hakan yasa ta kasa tabuka abin azo a gani yayinda koci Joseph Pep Guardiola ya baiwa wasu matasan yan wasa damar buga wasan farko a Manchester City.
Aleksandar Isak ne ya zurawa Newcastle kwallo a ragar City a minti na 53 bayan dawowa hutun rabin lokaci.
A wani labarin na daban victor Osimhen ya yi barazanar kai karar Napoli kan bidiyonsa da suka yada a kafar Tik Tok.
Wakilin Osimhen ya ce dan wasan zai iya kai karar Napoli gaban kotu bayan da aka buga wani faifan bidiyon Osimhen yana bugun fanareti sannan kuma aka goge shi daga shafin kungiyar na TikTok.
Bidiyon dai yana yin shagube akan dan wasan na Najeriya bayan ya kasa jefa kwallo.
Osimhen na Napoli ya taimaka wa kungiyar ta Italiya ta sami nasarar lashe kofin Serie A ta hanyar zura kwallaye 31 a kakar wasan da ta gabata.
Wakilin dan wasan na Najeriya Roberto Calenda ya fitar da wata sanarwa a shafin X yana mai cewa bidiyon ya haifar da mummunan lahani ga dan wasan.
Mun tanadi hakkin daukar matakin doka da duk wani shiri mai amfani don kare Victor inji Calendar.
Source LEADERSHIPHAUSA