Najeriya da Saudiyya sun buga canjaras a wasan sada zumunta da suka buga a kasar Portugal.
Wasan wanda ya ja hankalin masu kallon kwallo an tashi da ci 2 da 2.
Kungiya Ta Yi Allah Wadai Da Wallafa Hoton Gwamna Uba Sani A Cece-ku-cen Rabon Mukaman Siyasa
Salman Al Faraj ne ya fara jefa wa kasar Saudiyya kwallo a raga kafin Abdullahi Al Amri ya ci gida.
A minti na 81 dan kwallon tawagar Najeriya Kelecho Iheanacho ya jefa kwallo a ragar Saudiyya kafin Muhammad Kanno ya farkewa kasarsa a mintunan karshe na wasan.
A wani labarin na daban gwamnatin jihar Bauchi ta soke nadin Mista Aminu Umar, shugaban kungiyar riko na kungiyar kwallon kafa ta WIkki Tourists Football Club (FC), ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Muhammed Salis Gamawa, kuma ya bayyana wa manema labarai ranar Laraba a Bauchi.
“Ina sanar da ku shawarar da muka yanke na dakatar da aikinku na rikon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourists, wanda zai fara aiki nan da nan (yau).
“Nadin da aka yi muku a matsayin shugaban rikon kwarya don tafiyar da kungiyar ta hanyar da ta dace.
“Duk da haka, mun lura da jerin ayyuka da suka saba wa ka’idojin da aka bayar don gudanar da kungiyar yadda ya dace.
“An aikata abubuwan da suka haifar da cikas ga rikon amana da ingantaccen shugabanci da muke sa rai a kungiyar.
“Saboda haka, ba mu da wani zabi illa mu soke shugabancinku na wucin gadi,” in ji kwamishina.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba da kokarin da shugabannin suka yi a kungiyar tare da jajircewa wajen samun nasarar kungiyar.
“Duk da haka, dole ne mu kiyaye ka’idojin shugabanci nagari, kula da harkokin kudi da kuma bin ka’idojin da aka kafa.
“Mun yi imanin cewa wannan shawarar za ta zama wata dama a gare ku da kungiyar don sake tantancewa da ci gaba ta hanyar da ta dace da gaskiya da kwarewa,” in ji shi.
Sai dai Salis ya yi wa Umar fatan alheri a rayuwarsa ta gaba, tare da fatan zai ci gaba da bayar da gudunmawa ga harkokin wasanni.
Source LEADERSHIPHAUSA