Da alama Mufti Menk ya bibiyi wasan karshe na gasar cin kofin Duniya tsakanin kasar Argentina da Faransa Shehin ya zo Twitter ya rubuta: “Sannu da kokari Qatar, sannu da kokari Messi, sannu da kokari Mbappe…”
Mufti Menk ya yi wannan magana a lokacin da wasu malaman musulunci suke haramta wasan kwallon kafa.
Mufti Menk ya taya kasar Argentina da kuma kyaftin din ta, Lionel Messi murnar lashe gasar cin kofin Duniya wanda aka kammala a jiya.
Mufti Menk wanda ya yi suna wajen yin wa’azi a kasashen Duniya, ya yi amfani da shafin Twitter, ya aika sakon murna ga wadanda suka yi nasara.
Sa’o’i kadan bayan an kammala wasan karshe tsakanin Argentina da kasar Faransa, sai malamin musulunci ya yi rubutu a dandalin sada zumuntar.
Aminiya ta ce malamin ya yabawa kasar Qatar da ta shirya gasar shekarar nan, sai kuma ‘dan wasan gaban Argentina watau Lionel Messi.
Sai kuma Kyllian Mbappe Har ila yau, Mufti Menk mai shekara 44 ya yabi ‘dan wasan gaban Kasar Faransa, Kyllian Mbappe wanda ya zura kwallo uku a raga a wasan karshe.
A karshe Shehin ya yaba da kokarin da Argentina tayi wajen lashe kofin a karon farko tun 1986.
“Sannu da kokari Qatar, sannu da kokari Messi, sannu da kokari Mbappe, sannu da kokari Argentina!
A wannan jerin. Ina taya ku murna.” – Mufti Menk
Shehin malamin mai mabiya fiye da kusan mutum miliyan 10 ya kan yi magana a kan abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma a shafinsa na Twitter.
Zuwa karfe 2:00 na ranar Litinin, fiye da mutane 3000 suka maimaita abin da Mufti Menk ya fada, mutane 29, 000 suka nuna maganar ta ba su sha’awa.
Saudi Arabia v Argentina
Legit.ng Hausa ta fahimci a lokacin da Saudi Arabiya ta doke kasar Argentina a wasansu na farko a gasar, malamin addinin ya yi magana a Twitter.
A karshen watan Nuwamba, Mufti Menk ya nuna abubuwa sun jagwalgwalewa Messi da kasarsa, sannan ya jinjinawa kokarin ‘yan wasan Saudiyya.
Ronaldo ya yaba
A wani jawabi da ya yi a Twitter ranar Lahadi, an ji labari Ronaldo Luis Nazario de Lima ya yabi Lionel Messi wanda shi ne Kyaftin din kasar Argentina.
Ronaldo yana ganin ‘Dan wasan mai shekara 35 ya ba marada kunya, ya yi kwallon da babu wanda zai iya yi masa adawa a Duniya a gasar da aka buga.