Morocco ta yi samu nasara inda ta doke Tanzaniya da ci 3-0 a rukunin F a filin wasa na Laurent Pokou a ranar Laraba.
Kyaftin Romain Saiss ne ya zira kwallon farko gab da lokacin zuwa hutun rabin lokaci, inda Azzedine Ounahi da Youssef En-Nesyri suka kara kwallo biyu a ragar Tanzaniya.
Morocco ta ci gaba da taka leda inda ta samu galaba akan takwararta acikin fili, Tanzaniya dama biyu kacal ta samu amma ta gaza cin moriyar damar.
Tanzaniya ta shiga rudani yayin da Novatus Miroshi ya samu jan kati a minti na 70.
A wani labarin na daban tshon kyaftin din tawagar Super Eagles, John Mikel Obi, ya ce babu wata makawa ga tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles idan har suna son lashe gasar cin kofin Afrika (AFCON) da ke gudana a kasar Ivory Coast ta shekarar 2023.
Mikel, wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan Super Eagles da suka yi nasara a shekarar 2013 da suka lashe kofin AFCON na karshe a tawagar Nijeriya da ka buga a kasar Afrika ta Kudu, yayin da yake zantawa da LEADERSHIP a zauren taron bayar da zakaran dan kwallon duniya na FIFA na 2023 a birnin Landan na kasar Birtaniya a ranar Litinin, ya ce, in Super Eagles suna son lashe gasar ta bana, ba makawa, dole su doke tawaga mafi hatsari a gasar.
“Dole ne mu kara gyara kanmu, dole mu kara habaka kanmu, mun taka rawar gani a 2013 don lashe gasar, mun doke kasar Ivory Coast don cin nasara a gare su, dole ne tawagar Super Eagles ta maimaita tarihi. Idan suna son lashe gasar ta bana, dole ne su doke kasa mafi hatsari a gasar” inji shi.
Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea ya umarci Super Eagles da su yi imani da iyawarsu tare da sadaukar da kai yayin da suke daga tutar Nijeriya a kasar ta Ivory Coast.
Tawagar Super Eagles a wasanta na farko a wasanni gasar lashe kofin Afrika (AFCON) 2023 da ake bugawa a kasar Ivory Coast, ta buga canjaras da kasar Equatorial Guinea inda aka tashi 1:1, a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 6:00 na yanma, Nijeriya za ta sake buga wasa na biyu da mai masaukin baki – Ivory Coast.
Source: LEADERSHIPHAUSA