Tun a shekarar data gabata aka fara danganta dan wasa Leonel Messi da sake komawa tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona wadda ya shafe shekara da shekaru yana buga mata wasa a tarihin kwallon kafar sa. Yarjejeniyar da ke tsakanin Paris St Germain da Lionel Messi za ta kare a karshen kakar bana wanda hakan yake nufin kwantiraginsa zai kare a PSG, idan kungiyar ta lashe Ligue 1 a karshen kakar wasa ta bana.
PSG tana matakin farko a kan teburi da maki 66 da tazarar shida tsakaninta da Lens, wadda take ta biyu, bayan kammala karawar mako na 29 kuma tun da aka shiga kakar wasa ta 2023, Messi yake taka rawar gani,
wanda ya ci kwallo shida a wasanni 10, amma ya kasa cin Bayern Munich a gasar zakarun turai na Champions League.
Tuni aka fitar da PSG daga Champions League a kakar nan da French Cup, kenan Ligue 1 ne kadai a gabanta da take fatan dauka kawo yanzu amma kuma PSG ta ce a shirye take ta tsawaita zaman kyaftin din na Argentina a kungiyar.
Dan wasan mai shekara 35 shi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye inda ya zura kwallaye 672 a wasanni 778 da ya yi mata kuma Messi ya bar Barcelona a shekarar 2021, bayan da Barcelona ta fada matsin tattalin arziki, da ya sa dole a sayar da shi a kungiyar.
Messi ya dauki Champions League hudu a Barcelona da La Liga 10 da Ballon
d’Or shiga a kungiyar ta Sifaniya sai dai ya amince da kunshin yarjejeniyar kakar wasa biyu da rage masa albashi, amma hakan bai hana shi barin kungiyar da ya fara tun yana yaro ba.
Wasu rahotanni na cewar Barcelona ta tattauna da PSG kan batun Messi ya sake komawa Camp Nou da buga wasa a badi amma batun da ake na binciken Barcelona kan kudin da ta biya tsohon mataimakin kwamitin alkalan wasa na Sifaya ka iya hana shi kowawa dan kada ya fada ruduni.
Ana binciken Barcelona a Sifaniya da Uefa kan biyan kudi ga alkalin wasa, domin samun sakamakon wasa da zai amfani kungiyar sai dai Barcelona ta musanta aikatawa.
Messi wanda ya lashe kofin duniya a Katar a shekarar 2022, ya ci kwallaye sama da 100 a tawagar kasar Argentina, sannan ya haura sama da 800 da ya ci a tarihinsa na buga kwallo.