Shahararren dan wasan kwallon kafar nan na duniya Lionel Messi ya lashe kofinsa na farko a da tawagar kwalon kafar kasarsa bayan da kwallo daya tilo da Angel Di Maria ya saka a raga ya ba Argentina nasara 1-0 a kan masu masaukin baki Brazil a wasan karshe na gasar cin kofin Copa America da ya gudana ranar Asabar.
Wannan nasararta a filin wasa na Maracana a Rio de Janneiro na kasar Brazil ya kawo karshen zama na shekaru 28 babu wani babban kofi da Argentina ta yi, kana ya kawo karshen kwanaki dubu 2 da dari 5 da Brazil ta yi ba a doke ta a gida ba.
Rabon Argentina da lashe wata babbar gasa tun a shekarar 1993, lokacin da kwallaye 2 da shahararren dan wasanta Gabriel Batistuta ya ci suka ba ta nasara a kan Mexico a wasan karshe na Copa a kasar Ecuador.
Kuma yayin da Messi mai shekaru 34 ya kawo karshen rashin lashe babban kofi a kasarsa, Neymar dan kasar Brazil, wanda ya ke kasa da Messi da shekaru 5 ba shi da wani babban kofi da ya lashe da tawagar kasarsa, bayan da Brazil ta lashe kofin babu shi, shekaru 2 da suka wuce saboda rauni da ya samu.
Di Maria ya ci wa Argentina kwallonta ne a minti na 22 da fara wasan, kuma ita ta makale har aka tashi.