Fitaccen ɗan wasan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi ya kulla yarjejeniya da PSG ta kasar Faransa Ɗan wasan zai sanya hannu a kan yarjejeniyar shekara biyu tare da damar tsawaitawa zuwa uku Messi ya bayyana karara cewa baya son barin tsohuwar kungiyarsa Barcelona kuma ya yi duk me yuwuwa domin cigaba da zama France.
Shahararren ɗan wasan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi, ya amince da yarjejeniyar shekara 2 da kungiyar Paris Sait-Germain.
Ɗan wasan wanda ya bar tsohuwar kungiyarsa Barcelona a makon da ya gabata ya samu ta yi guda biyu amma ya zaɓi tafiya PSG ta kasar Faransa. Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallo na duniya Ballon d’Or sau shida zai kwashi kuɗi kimanin £25m duk shekara bayan cire haraji.
Jaridar kwallo ta Skysport ta ruwaito cewa: “Kungiyar PSG da sabon ɗan wasan nata Messi suna da zaɓin tsawaaita zamansa a babban birnin Faransa da shekara ɗaya, yayin da ɗan wasan zai samu tagomashin £25m na sanya hannu.”
Meya dakatar da Messi tsawaita zamansa a Barcelona? BBC Hausa ta rahoto ɗan kwallon na Argentina ya shirye tsawaita zamansa na shekara 21 a Barcelona inda ya amince a zaftare kashi 50 cikin dari na albashinsa. Sai dai a ranar Alhamis kungiyar Barcelona ta sanar cewa matsalolin kudi da dokokin gasar La Liga sun hana ta tsawaita kwangilar Messi.
Jawabin bankwana Fitaccen ɗan wasan mai shekara 34 a duniya ya bayyana cewa yana son zama a Barcelona kuma ya yi duk mai yiwuwa domin cigaba da zaman nasa.
Messi ya fashe da kuka yayin jawabin bankwana ga magoya bayan ƙungiyar Barcelona, inda ya bayyana musu yana fatan watarana zai dawo kungiyar.
A jawabin bankwana da ɗan wasan ya yi ranar Lahadi, ya godewa magoya bayan kungiyar Barcelona bisa nuna soyayyarsu garesa a kowane lokaci.