A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta tabbata cewa ta fadi daga gasar Firimiyar Nijeriya bana duk da nasarar da ta samu a wasanta na karshe akan Shooting Stars da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a nan Kano.
Wannan dai shi ne karo na uku da kungiyar ta fada ajin gajiyayyu a tarihi tun bayan kafa ta a shekarar 1990, Kano Pillars dai ta taba faduwa daga gasar Firimiya a shekarar 1994 da 1999, sai kuma wannan karon.
‘Yan Sandan Birnin Milan Sun Ba Wa Dan Wasa Bukayoko Hakuri
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dai ta taba lashe gasar firimiyar Nigeriya sau hudu inda ta lashe a shekarar 2008 da 2012 da 2013 sai kuma kakar wasa ta 2014, sannan a shekarar 2019 ta lashe gasar Aito Cup.
Kano Pillars tana da tarihi a fagen kwallon kafa a Nigeriya da kuma nahiyar Afirka, inda ko a shekarar 2009 sai da kungiyar ta samu damar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Sai dai me ya sa Pillars din ta fada ajin gajiyayyu?
Rashin Kwararren Shugaba
Mutane da dama dai suna ganin shugaban kungiyar, Surajo Yahaya Jambul, wanda aka dakatar, bashi da cikakkiyar kwarewar da zai iya jan ragamar kungiyar hart a samu irin ci gaban da ake bukata musamman saboda rashin kwarewarsa akan harkokin wasanni.
Kano pillars dai ta taba rike mukamin Kungiyar kwallon kafa mafi kwarjini da farin jini a arewacin Najeriya dama wasu yankuna na kudancin Najeriya.
Source: Leadership