Dan wasan PSG Kylian Mbappe yayin murnar zuru kwallo a wasan karshe da suka kara da Monaco ranar 9 ga watan Mayu 2021.
Dan wasan PSG Kylian Mbappe yayin murnar zuru kwallo a wasan karshe da suka kara da Monaco ranar 9 ga watan Mayu 2021. FRANCK FIFE AFP
Shugaban kungiyar Paris Saint – Germain na kasar Faransa Nasser Al-Khelaifi ya kawo karshen duk wasu zantuka dake alakanta batun sayar da gwarzon dan wasan gaba na kungiyar Kylian Mbappe.
Da yake shaidawa jaridar L’Equipe, Al-Khalifi yace, Mbappe zai ci gaba da kasancewa daram a babban birnin Faransa wata Paris, yana mai cewa, basu da niyyar sayar da Mbappe, hasalima dan wasan bazai koma ko ‘ina a kyauta ba.
Dan wasan París Saint-Germain Kylian Mbappe lokacin sarrafa tamola yayin wasa ranar 28 ga watan Afrilu 2021
Dan wasan París Saint-Germain Kylian Mbappe lokacin sarrafa tamola yayin wasa ranar 28 ga watan Afrilu 2021 Anne-Christine POUJOULAT AFP
A watan Yuni shekarar 2022 ya kamata kwantiragin Mbappe ya kare, kuma ansha alankata shi da komawa kungiyar Real Madrid dake Spain.
Barcelona bata kudin sayen Neymar
Shugaban na PSG yayi kuma tsokaci dangane da batun komawar Neymar Junior zuwa Barcelona, inda yace kungiyar ta Katolonia bata da kudin sayen dan wasan a yanzu, hasalima dan wasan bashi da niyyar yiwa tsohowar kungiyarsa kome.
A wani labarin cigaban wannan annobar cutar korona ta kawo cikas a wasannin nahiyar afrika dama sauran sassan duniya .
Kamar yadda hukumar wasanni ta afirka ta sanar an dage gudanar da wasannin kakar wasanni ta wannan shekarar sakamakon barkewar cutar korona a kasar kamaru inda aka sanya za’a gudanar da wasannin.
Majiyar mu ta tabbatara mana ta cewa ana sa ran kasar afrika ta kudu ta samu damar karbar bakuncin kakar wasannin ta bana sakamakon dauke gasar daga kamaru da akayi.
Idan hakan ta tabbata ana sa ran a sanar magoya bayan kwallon kafa zuwa sati mai shigowa.