‘Yan wasan matan Super Falcons dake wakiltar Najeriya a gasar cin Kofin Duniya da ake bugawa a kasar Australia sun buga canjaras da kasar Canada a wasan farko.
Mai tsaron gida Chiamaka Nnadozie ita ce jaruma yayin da bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta yi a minti na 50 ta tabbatar da cewa Super Falcons ta Najeriya ta samu maki a bugun daga kai sai mai tsaron gida a rukunin B na gasar cin kofin duniya ta mata da suka yi da Canada.
Kungiyoyin biyu sun samu damarmakin da suka kasa amfani dasu a wasan da duk wanda ya zura kwallo daya ta isa ya lashe wasan.
Damar da Najeriya ta samu a zagayen farko ta fito ne daga Ifeoma Onumonu wanda bugun daga kai sai mai tsaron gida ya tilasta mai tsaron gidan Canada tsalle sama.
Oshoala kuma ta samu damar jefa kwallo amma ta kasa yin amfani da kuskuren da mai tsaron ragar Canada ta yi.
Da mintuna biyu kacal da fara wasan, Francisca Ordega ta yi wa Christine Sinclair keta a cikin da’ira ta 20 abin da ya bai wa yan kasar Canada dama.
Nnadozie, duk da haka, tay kokari sosai don dakatar da ƙoƙarin Sinclair na jefa kwallo a bugun tazara.
Yar wasan matan Najeriya Deborah Abidoun wacce ta yi fice a gasar cin kofin duniya ta farko ta fita daga filin wasan bayan da aka nuna mata jan kati kai tsaye kan laifin da ta yi wa Ashley Lawrence ta Canada.
Yan wasan na Randy Waldrum za su kara da Australia mai masaukin baki a ranar 27 ga Yuli.