Manyan kungiyoyi a Ingila na rububin Depay, Tottenham na son sabon gola
Manchester United da Newcastle da Arsenal har ma da Chelsea, sun nuna sha’awar sayen dan wasan Netherlands, Memphis Depay, wanda ake sa ran zai bar Barcelona cikin wannan Janairun nan.(Sport).
A wata mai kama da haka kuwa Arsenal ta nuna sha’awar sayen matashin dan wasan Barcelona Alejandro Balde, in ji Sport.
Newcastle kuwa Moussa Diaby ta ke son daukowa daga Bayern Leverkusen idan kaka ta kare.(Bild)
Sai kuma Aston Villa wadda dab take da sayen mai tsaron bayan Sfaniya da Real Betis, wato Alex Moreno, a cewar Bild.
Southampton kuwa na duba yiwuwar dauko dan wasan gaban Japan, Daizen Maeda da ke wasa a Celtic.(Sky Sports)
Shi kuwa daraktan wasanni a Roma Tiago Pinto, na da kwarin gwuiwa cewa mai tsaron bayan Ingila Chris Smalling zai tsawaita zamansa da kungiyar.(Football).
A Sfaniya kuwa, Atletico Madrid na son sake saye tsohon dan wasanta Alejandro Garnacho, da yanzu ke wasa a Manchester United.
To amma rahotanni sun ce da wahala United ta yadda matashin ya bar Old Trafford.(Fichajes)
Akwai kuma rahotannin da ke cewa Man United din na duba yiwuwar sayen Edin Dzeko na Inter Milan, wanda ya samu nasara zamansa a Manchester City.(Mail)
Sai kuma Tottenham da ke sa ido ga golan Brentford David Raya mai shekaru 27, don ya maya gurbin Hugo Lloris na tsawon lokaci.( Telegraph).