Sir Jim Ratcliffe zai biya fam biliyan 1.3 domin sayen kashi 25 cikin 100 na Manchester United bayan da babban dan kasuwan kasar Qatar Sheikh Jassim bin Hamad al Thani ya janye daga cinikin.
Tayin da Sheikh Jassim ya gabatar, wanda ya kai darajar Manchester United sama da fam biliyan 5 shi ne kawai tayin mallakar kashi 100 na kungiyar.
Amma duk da hakan bai sa masu kungiyar Glazers Family wadanda suka mallaki United tun 2005 suka sallama ba,don haka Sheikh Jassim ya janye daga cinikin kungiyar.
Amma duk da haka Glazers sun amince su sayarda kashi 25 cikin 100 na kungiyar ga hamshakin dan kasuwar kasar Amurka Sir Jim Ractlife,inda ake sa ran kai karshen yarjejeniyar a wani zama da mahukuntan kungiyar zasu yi a wannan makon.i
A wani labarin na daban filin wasa na Municipal de Portimao dake kasar Portugal na shirin karbar bakuncin wasan sada zumunci na kasa da kasa tsakanin Saudiyya da Nijeriya a ranar Juma’a, 13 ga watan Oktoba, 2023.
Nijeriya zata buga wasan ne bayan ta samu nasara akan Sao Tome & Principe da ci 6-0 a watan Satumba.
Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen shi ne ya fi fice a cikin yan wasan Nijeriya da zasu hadu da Saudiyya.
Bayan da Super Eagles ta samu nasara a kowanne wasa ukun da ta buga na baya bayannan, za ta yi kokarin ganin ta ci gaba da taka rawar gani a karawar da zata yi da Saudiyya.
Sau daya ne Saudiyya da Nijeriya suka kara a matakin kasa da kasa a wasan sada zumunci a gabanin gasar cin kofin duniya ta 2010, inda suka tashi babu ci a filin wasa na Abuja.
A kididdigar da FIFA ta fitar, Nijeriya tana matsayi na 40 yayinda Saudiyya take matsayi na 57 a iya taka leda a Duniya.
Source LEADERSHIPHAUSA