Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kara farashin da ta ke son sayen Jadon Sancho daga Borussia Dortmund zuwa yuro miliyan 85 da nufin kawo shi Old Trafford a sabuwar kakar wasan da za ta faro.
Kafin yanzu dai Sancho mai shekaru 21 ya ki amincewa da tayin United ko da ya ke akwai tsammanin ya amince a wannan karon duk da gibin yuro miliyan 10 kan farashin da kungiyar tasa mai doka Bundesliga ta sanya akanshi.
Jadon Sancho wanda ke cikin tawagar Ingila da ke doka wasannin gasar Euro yanzu haka, matukar ya amince da tayin na United kai tsaye Club din nasa zai iya sakinsa bisa tanadin hakan karkashin kwantiragin da ke tsakaninsu.
Duk da cewa dan wasan bai yi wata rawar gani a wasannin na Euro ba amma ya nuna matukar bajinta cikin kakar da ta gabata karkashin wasannin Lig.
A baya-bayan nan Sancho dan Ingila, na da kwallaye 50 a wasanni 137 da ya dokawa Borussia Dortmund yayinda a bangare guda ya dokawa kasarsa wasanni 20 ya kuma zura kwallaye 3.
Tun bayan da Dortmund ta sayo shi daga Manchester City a 2017 kan yuro miliyan 10, ya taimaka wajen zura kwallaye 109 ciki har da 2 da ya zura a karawarsu a RB Leipzig wanda ya basu damar lashe kofin Jamus.
Manchester united na cikin manya manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa a nahiyar turai kuma ana sa ran zasu sayi ‘yan waasa da yawa a wannan lokaci domin tunkarar kakar wasanni ta gaba wanda za’a tunkara.
Kungiyar tana da kudin shigar da suka kai miliyoyin daloli inda ake sanya ta cikin kungiyoyin kwallon kafa masu karfin tattalin arziki a nahiyar turai.