Manchester City ta shirya don zaffa neman dan wasan Totenham Harry Kane, inda yanzu haka kungiyar, wadda ita ta lashe gasar Firimiya tana shirye shiryen taya dan wasan hukumance.
Akwai rade radi daga majiyoyi kusa da kungiyar ta City da ke nuni da cewa kungiyar ta yi tayin biyan fam miliyan 100 a kan dan wasan, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 139.
Sai dai abin da ke dahir shine Manchester City na matukar bukatar dan wasan gaban na Ingila mai shekaru 27, duba da yadda Koch Pep Guardiola ya zaku ya sanya shi a cikin tawagarsa da ta lashe gasar Firimiya ta kuma kai wasan karshe na zakarun nahiyar Turai.
yanzu haka dai Harry Kane yana da sauran kwantiragi da kungiyar Tottenham da zai kai har shekarar 2024.
A wani labarin na daban mai kama da wannan dan wasan gaba na kwallon kafar Ingila, Harry Kane na ci gaba da jagorantar fafutukar lashe kyautar dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ta bana da ke gudana a Rasha.
Idan har burin Harry Kane ya tabbata, zai zama dan wasan Ingila na farko da ya samu wannan kyauta, bayan makamancin tarihin da dan wasan kasar ta Ingila Gary Lineker ya kafa shekaru shekaru 32 da suka gabata.
A gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986 ne Lineker ya ci wa Ingila kwallaye shida a wasannin da ya buga mata, abinda ya bashi damar lashe kyautar dan wasa mafi yawan kwallaye a gasar.
Yayinda da gasar cin kofin duniya ta bana ke gudana a yanzu aka, Harry Kane yana da kwallaye 6, wadanda ya samu zurawa a wasannin da Ingila da buga da kasashen Tunisia, Panama da kuma Colombia.